Za'a rantsar da shugabannin kwamitocin majalisar dattawa a ranar Laraba - Sanata Lawan

Za'a rantsar da shugabannin kwamitocin majalisar dattawa a ranar Laraba - Sanata Lawan

A gobe Laraba, 25 ga watan Satumban 2019, za a rantsar da sabbin shugabannin kwamitocin majalisar dattawa da aka nada kamar yadda shugaban majalisar, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan ya bayyana.

Jaridar PM News ta ambato Sanata Lawan a yayin bayyana wannan sanarwa yayin zaman majalisar da aka gudanar a yau Talata, 24 ga watan Satumba bayan hutun da ta shiga tun a watan Yuli.

Sanata Lawan ya yi bayanin cewa, majalisar bayan tafka muhawara a kan matsalolin da suka shafe ta da kuma majalisar tarayya baki daya, ta kuma yanke shawarar rantsar da sabbin shugabannin kwamitocinta a zaman sirri da ta gudanar na tsawon sa'a daya.

Ana iya tuna cewa, majalisar dattawan Najeriya gabanin shigar ta hutu a ranar 30 ga watan Yulin 2019, ta tattauna a kan batun gabatar da kasafin kudin kasa na 2020.

KARANTA KUMA: Bani da wata faduwar gaba kan barazanar tsige ni - Trump

Rahotanni sun bayyana cewa, majalisar a yayin zaman da za ta gudanar na ranar Laraba, za ta tafka muhawara dangane da hukuncin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanke na rufe iyakokin kasa na kasar nan.

Hakan na zuwa ne biyo bayan shiftar da Sanatan shiyyar Kebbi ta tsakiya, Adamu Aliero yayi wajen jan hankalin abokanan aikinsa dangane da kyakkyawan tasirin da hukuncin shugaba Buhari ke ci gaba da yi ta fuskar magance shigo da kayayyaki na fasakwauri cikin kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel