An kama sojoji 7 da aka kora cikin kungiyar 'yan fashi da makami

An kama sojoji 7 da aka kora cikin kungiyar 'yan fashi da makami

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Legas ta ce ta kama wasu sojoji da aka kora daga aiki tare da wasu 'yan kungiyar fashi da makami da a suka yi wa mazauna unguwar Ijegun fashi sanye da kayan sojoji a cewar kwamishinan 'yan sanda Zubairu Mua'azu a jiya Litinin.

Ya ce a watannin baya-bayan nan da suka shude, rundunar ta kama wadanda ake zargi da fashi da makami 40, 'yan kungiyar asiri 29 da wadanda suka aikata kisar gilla 19. Ya kara da cewa rundunar da dakile fashi da makami 31 an kuma kwato bindigu 19 da alburusai 51 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wadanda ake zargin sun hada da sojojin kasa uku da aka kora, sojojin ruwa biyu da farar hula biyu. Muazu ya ce sojojin sun hada da Ndidi Oluchukwu, 30; Owolabi Adeyemo ,42; David Olufemi, 47; Iseyin Samuel Isreal, 41; Emeka Ibeh, 29, Samuel Anochime, 36, da Ebedot Stephen, 27 da ake zargi da fashi da makami da satar mota.

DUBA WANNAN: Yadda yarjejeniya da aka kulla tsakanin tsohon gwamnan PDP da Buhari kafin zabe ta samu tangarda

Shugaban 'yan sandan ya ce an kama wadanda ake zargin ne bayan sun yi wa wani mutum fashin motarsa kirar Lexus RX33o a ranar 18 ga watan Fabrairu a hanyarsa ta zuwa Ijegun bayan da ya baro Ibadan.

Abubuwan da aka kwato wurin wadanda ake zargin sun hada da kayan sojoji guda 12, katin shaida na soji guda 12, adduna biyu, katin ATM da dama, wukake, dan kampai na mata da zobe.

Kwamishinan 'yan sandan na Legas, Zubairu Mu'azu ya ce wadanda ake zargin sun amsa cewa sun aikata fashi da makami da yawa a garin Ijegun da kewaye. Ya ce za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel