Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An bude sabon Masallaci na 'Yan Luwadi da Madigo a yankin Turai

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An bude sabon Masallaci na 'Yan Luwadi da Madigo a yankin Turai

- Wani limami a birnin Melbourne na kasar Australia ya bude sabon Masallaci na 'yan Luwadi da Madigo

- Limamin mai suna Imam Nur Warsame shine limami na farko da ya fara fitowa a duniya ya bayyana cewa shi dan luwadi ne

- Limamin ya bayyana cewa zai bude wannan masallaci ne saboda ya zama wajen ibada, ya kuma zama tamkar wajen kariya ga 'yan luwadi da madigo

Limamin 'yan luwadi Nur Warsame ya bayyana kudurinsa na bude sabon Masallaci a kasar Australia da zai yi maraba ga dukkanin 'yan luwadi da 'yan madigo domin su dinga zuwa suna ibadarsu sannan kuma ya zama wajen kariya a garesu.

Limamin wanda kowa ya san cewa shi dan luwadi ne, ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne bayan, korafin da yake ta faman samu a wajen Musulmai 'yan luwadi da madigo wadanda suke ganin basu da wajen buya akan irin barazanar da suke samu.

Warsame dai shine babban limamin wani Masallaci a birnin Melbourne na kasar Australia, kuma shine limami na farko da ya fara fitowa ya nuna cewa shi dan luwadi ne a shekarar 2010, tun lokacin kungiyoyin Musulmai suka fara sukar shi.

KU KARANTA: Tirkashi Shekarau na tsaka mai wuya: Kotu za ta hana Shekarau, Aminu Wali da wasu mutane fita daga Najeriya

Warsame ya kara da cewa da yana da aure, amma kuma sai yaga ba zai iya cigaba da zama da matar ba. Yanzu haka an hana shi zuwa Masallaci, ya ce yana so ya gina wannan Masallaci ne a Melbourne domin ya zama wajen ibada, kariya da kuma kawo korafi ga Musulmai 'yan luwadi da madigo.

Imam Warsame ya ce: "Wannan abu ne da yake da matukar muhimmanci ga Musulmai 'yan luwadi da madigo, wadanda suke zaune cikin tsoro da fargaba saboda kawai sun fito sun nuna akidarsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel