Yan majalisar dokokin jihar Sokoto 2 sun yi gagarumin nasara a kotun zabe

Yan majalisar dokokin jihar Sokoto 2 sun yi gagarumin nasara a kotun zabe

Kotun da ke sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin jihar Sokoto, a ranar Litinin, 23 ga watan Satumba tayi watsi da karar da aka shigar akan mambobin majalisa da ke wakiltan mazabun Sabon Birni Kudu II da Sokoto ta Kudu II a majalisar jihar.

Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben mazabar Sabon Birnin Kudu II, Adamu Gado Gatawa ya shigar da kara inda yake kalubalantar zaben Sa’idu Neno Ibrahim na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A daya bangaren kuma dan takarar APC a zaben mazabar Sokoto ta Kudu II, Aminu Garba Gidadawa ya shigar da kara akan zaben Mohammed Malami Ahmed na PDP.

A kararsa, Gatawa yayi ikirarin cewa Ibrahim bai cancanci takarar zaben ranar 9 ga watan Maris, 2019 ba inda yayi zargin cewa mai mallaki ilimin sakandaren da ake bukata ba.

Ya kuma yi zargin cewa zaben bai bi ka’idar dokar zaben kasar ba, sannan cewa Hon. Ibrahim bai samu yawan kuri’un da ake bukata bisa doka ba.

Da yake yanke hukunci, Justis Hamman Idi Polycap, yake karar bai da inganci.

Yayi bayanin cewa mai karar ya gaza tabbatar da zargin fiye da tsammani.

KU KARANTA KUMA: Babu wata matsala Dan kujerar shugaban kasa ta cigaba da zama a arewa a shekarar 2023 - Ango Abdullahi

Hakazalika, Justis I. Iwodi wanda ya yanke hukunci akan karar Aminu Garba Gidadawa akan zaben Mohammed Malam Ahmed yayi watsi dashi kan rashin inganci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel