Kelechi Iheanacho ya shafe shekara guda bai jefa kwallo a raga ba

Kelechi Iheanacho ya shafe shekara guda bai jefa kwallo a raga ba

A cikin karshen makon da ya gabata ne babban ‘Dan kwallon kungiyar Super Eagles na Najeriya, Kelechi Iheanacho, ya cika shekara guda cir bai iya jefa kwallo ko da guda a cikin raga ba.

Kelechi Iheanacho mai bugawa Super Eagles ya dauki watanni 12 ba tare da ya iya cin kwallo a kungiyarsa ta Leicester City da ke kasar Ingila ba. Rabonsa da kwallo a Turai tun Satumban bara.

‘Dan wasan gaba Iheanacho ya ci kwallonsa ta karshe a kulob din sa ne tun a cikin Satumban 2018 lokacin da Leicester City ta kara da kungiyar Huddersfield a kakar gasar Firimiyan baran.

Tun da Koci Brendan Rodgers ya karbi Leicester, ko sau daya bai taba sa Iheanacho ba. Ko a wasan Tottenham da kungiyarsa ta samu nasara, ‘dan wasan na Najeriya bai samu bugawa ba.

KU KARANTA: Najeriya za ta kece raini da 'Yan wasan kasar Brazil

Tauraron na Super Eagles ba zai so ya cigaba da tunawa da wannan mummunan tarihi da ya ajiye a gasar Firimiya ba. Wasanni 25 ke nan aka shafe ‘dan wasan gaban bai ci kwallo ko daya ba.

Matashin ‘dan wasa Iheanacho mai shekaru 22 ya dawo Garin Leicester ne daga Manchester a karshen kakar wasan shekarar 2019 inda aka saida shi a kan kudi kusan fam miliyan $30.

A cikin makon ne kuma Man City ta lallasa Watford da ci 8 da nema. Tun a cikin mintunan 20 na farko aka dirkawa Watford kwallaye 5. A tarihin gasar Firimiya, ba a taba ganin haka ba.

Bernardo Silva ya zura kwallaye 3 inda David Silva, Kun Aguero, Riyad Mahrez, Nicolas Otamendi da Kevin Bruyne su ka dauki ganima yayin da Watford ta gagara cin ko kwallo guda.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel