Ni zan zama Shugaban kasar Najeriya a 2023 – Inji Fasto Tunde Bakare

Ni zan zama Shugaban kasar Najeriya a 2023 – Inji Fasto Tunde Bakare

Babban Limami kum shugaban cocin nan na Latter Rain Assembly da ke Garin Legas, Fasto Tunde Bakare, ya bada tabbacin cewa shi zai zama shugaban kasar Najeriya a zabe na gaba da za ayi.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana daga jaridar Business Day ta kasar nan, Faston ya na cewa an nuna masa tafiyar siyasar kasar nan, kuma da zarar shugaba Buhari ya kammala mulki sai shi.

Babban Faston wanda ya san harkar siyasa ya ke cewa wadanda ba su da labari su sani cewa Muhammadu Buhari ne shugaban kasa na 15 a Najeriya, yayin da shi kuma zai zama na 16 a jerin.

Buhari ya sa hannusa ya dafa a kirji yana cewa: “Ina so ku san wannan a safiyar nan cewa babu abin da zai iya canza wannan kadara da sunan Ubangiji. Shi Buhari ne na 15; Ni kuma na 16.”

KU KARANTA: Mutanen Katsina ta Arewa su na so su fito da Gwamna a 2023

Malamin bai tsaya nan ba inda ya cigaba da cewa: “Saboda haka aka haife ni, kuma wannan ne ya kawo ni Duniya.” Tunde Bakare ya na maganar ya rike shugaban kasar Najeriya nan gaba.

Na yi shekaru 30 ina wannan tanadi. Lokacin da shi (Buhari) ya zabi ya yi takara a 2019, shi ne na 15, da zarar ya tafi, ni zan shigo. Aikin sa shi ne irin na Annabi Musa na zuwa gaban teku…"

…Ba zai iya karasa da mutanensa su tsallaka ruwa ba. Sai Yusha’u ya tafi dayan bangaren domin ya raba arzikin Najeriya ga mutanen kasar nan.” Faston ya ke fadawa Mamu a harshen Malamai.

Idan ku na biye da tarihi, Muhammadu Buhari ya taba tsayawa takara tare da Tunde Bakare a matsayin mataimakinsa. An yi wannan ne a zaben 2011 a karkashin tsohuwar jam’iyyar CPC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel