Yaki da ta’addanci: Har yanzu da makaman da Shagari ya siyo muke aiki – Sojojin Najeriya

Yaki da ta’addanci: Har yanzu da makaman da Shagari ya siyo muke aiki – Sojojin Najeriya

Wasu manyan kwamandojin rundunar Sojin Najeriya dake yaki da yan ta’addan Boko Haram sun koka kan rashin ingantattun makamai na zamani da zasu taimaka musu wajen gamawa da mayakan na Boko Haram a yankin Arewa gabas.

Rahoton jaridar The Cables ta gudanar ya ruwaito manyan kwamandojin sojin sun koka matuka game da halin da suke ciki, inda suka ce har yanzu suna amfani da tsofaffin makamai ne wanda tun zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Aliyu Usman Shehu Shagari aka sayo su.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta kammala shirin kaddamar da bincike a kan Kwankwaso da Wamakko

Dama dai majiyar Legit.ng ta taba ruwaito yadda Sojoji suke fama da karancin kayan aiki a yankin Borno, daga ciki har da karancin kayan sawa, inda har ta kai ga Sojoji suna amfani da silipas, suna kwana a cikin dakunan makaranta suna kuma rokon abinci.

Guda daga cikin kwamandojin yace: “Bindigun Shilka da muke amfani dasu an sayosu ne tun zamanin Shagari, akwaisu dayawa, amma fa sun tsufa, an daina yayinsu, amma aka yi musu kwaskwarima, aka kuma baiwa Sojoji dake yaki da ta’addanci, don haka suke lalacewa a dilin daga.

“A yayin da muke aiki da bindigar Shilka da aka yi ma kwaskwarima, mayakan ISWAP na amfani da makamai na zamani wajen kai mana hari, kuma ka san dama shugaban kasa ya yi magana a taron ECOWA makon daya gabata yana nuna damuwa da yadda Boko Haram ke amfani da makaman zamani.” Inji shi.

Shi ma wani kwamandan ya bayyana cew Sojoji an amfani da tankar yaki ta T-72 ne a filin daga, wanda yace a shekarar 1971 aka kerasu a kasar Rasha, kuma zuwa shekarar 1972 ma an karar dasu, amma har yanzu dasu Najeriya ke amfani.

“A zamanin Goodluck aka sayosu gab da zaben 2015, da su aka kwato garuruwan da Boko Haram ta kwace kafin zabe, sai dai matsalar shine sun zo Najeriya ba tare da sassan jikinsu da za’a iya canzawa ba idan wani bangare ya lalace ba.

“Sai dai mu cire sassan jikin wannan mu sanya ma wanda ya lalace, a haka dukansu sun mutu, don haka aka janyesu, a yanzu tankar yaki da muke amfani dashi shine Vickers MBT, wanda ya ma girmi T-72, don haka ga wannan matsalar, ga matsalar Shilka, shi yasa Boko Haram ke samun nasara.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel