Siyasar 2023: Zan fito takarar shugaban kasa – Dan majalisa Gudaji Kazaure

Siyasar 2023: Zan fito takarar shugaban kasa – Dan majalisa Gudaji Kazaure

Dan majalisar daga jahar Jigawa, dake wakiltar mazabar Roni, Kazaure da Yan kwashi, Honorabul Muhammad Gudaji Kazaure ya bayyana cewa mukamin dan majalisa ta mai kadan, don haka takarar shugaban kasa ce a gabansa.

Gudaji ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da gidan rediyon BBC Hausa, inda aka tambayeshi game da abin da yake ciki bayan bai samu nasara a kokarinsa na tsayawa takarar shugabancin majalisar wakilai ba.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta kammala shirin kaddamar da bincike a kan Kwankwaso da Wamakko

Amma Gudaji ya amsa cewa tun bayan da jam’iyyar APC ta bashi hakuri game da takarar kujerar kaakakin majalisar wakilai, shi ma ya hakura. “Na fidda rai, amma idan Allah Yasa an sake dawowa, toh sai inda karfina ya kare.”

Gudaji ya kara da cewa yana da burin tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya ko kuma takarar gwamnan jahar Jigawa domin ya samu daman taimaka ma talaka yadda ya kamata, saboda a cewarsa taimakon da yake yi ma talaka a kujerar dan majalisa ta yi kadan.

“Idan kuma na samu cigaba, yadda nake so shi ne takarar shugaban kasa ko kuma takarar gwamna, dan majalisar ma ni gani nake yi bana iya talaka wani abu sosai, amma can inda za’a kawo kayan talakawa, toh can ne nake ganin zan iya kaisu inda talaka zai amfana.

“Duk abinda gwamnati ta kawo da muke ganin zai iya ma talaka illa, indai muna nan zamu ce a’a, kana gani kwanan nan da babban banki suka kafa dokar ajiyar kudi cewar idan an kai ajiyan kudi za’a dinga cire wani abu muka mike muka ce bamu yarda ba.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Hukumar EFCC, za ta kaddamar da bincike a kan tsohon gwamnan jahar Kano, Rabiu Kwankwaso da tsohon gwamnan jahar Sakkwato, Aliyu Magatakarda Wamakko.

EFCC na tuhumar gwamnonin biyu da badakalar karkatar da kudade da kuma satar kudade a yayin da suke kujerar gwamna, inda take tuhumar Kwankwaso da karkatar da naira biliyan 3.08, shi kuma Wamakko tana tuhumarsa da satar naira biliyan 15.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel