Gwamnan Bauchi ya baiwa yaron Dahiru Bauchi wani babban mukami a gwamnatinsa

Gwamnan Bauchi ya baiwa yaron Dahiru Bauchi wani babban mukami a gwamnatinsa

Gwamnan jahar Bauchi, Bala Mohammed ya nada dan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Dakta Abubakar Sirinbai Dahiru Bauchi a matsayin sabon shugaban hukumar ilimi ta bai daya ta jahar Bauchi, watau Bauchi SUBEB, inji rahoton jaridar Blue Print.

Shi dai Dahiru Bauchi fitaccen Malamin addinin Musulunci ne dan asalin jahar Bauchi, amma mazaunin garin Kaduna da ya dade yana yi ma Musulunci hidima, kuma jagora ne a tafiyar darikar Tijjaniyya.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta kammala shirin kaddamar da bincike a kan Kwankwaso da Wamakko

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wata sanarwa daga ofishin sakataren gwamnatin jahar, Alhaji Sabiu Mohammed Baba ta bayyana cewa gwamnan ya nada Alhaji Yakubu Barau Ningi tare da Zakari Ibrahim Muhammad a matsayin kwamishinoni a kwamitin gudanarwa ta hukumar.

Sauran mambobin wannan kwamiti sun hada da Yusuf Abdullahi Itas, Abbas Waziri da Comfort Audu, kamar yadda gwamnan ya nadasu, daga karshe sanarwar ta kara da cewa nadin ya fara aiki nan take.

A wani labarin kuma, Hukumar EFCC, za ta kaddamar da bincike a kan tsohon gwamnan jahar Kano, Rabiu Kwankwaso da tsohon gwamnan jahar Sakkwato, Aliyu Magatakarda Wamakko.

EFCC na tuhumar gwamnonin biyu da badakalar karkatar da kudade da kuma satar kudade a yayin da suke kujerar gwamna, inda take tuhumar Kwankwaso da karkatar da naira biliyan 3.08, shi kuma Wamakko tana tuhumarsa da satar naira biliyan 15.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel