Hukumar EFCC ta kammala shirin kaddamar da bincike a kan Kwankwaso da Wamakko

Hukumar EFCC ta kammala shirin kaddamar da bincike a kan Kwankwaso da Wamakko

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta bayyana shirinta na kaddamar da bincike a kan tsohon gwamnan jahar Kano, Rabiu Kwankwaso da tsohon gwamnan jahar Sakkwato, Aliyu Magatakarda Wamakko.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito wani rahoto daga jaridar Daily Trust ne ya bayyana da haka, inda tace ana tuhumar tsofaffin gwamnonin biyu ne da tafka laifukan da suka shafi rashawa da badakalar kudade a zamanin mulkinsu.

KU KARANTA: Adanan Menderes: Mutumin da yayi ma Musulunci hidima yar ya rasa ransa a sanadiyyar haka

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya tabbatar da shirin nasu na fara binciken Sanata Kwankwaso, jagoran darikar Kwankwasiyya da kuma Sanata Aliyu Wamakko.

“Hukumar za ta binciki gayyaci Kwankwaso domin ta bincikesa a kan tuhumarsa da ake yi da karkatar da makudan kudade da suka kai naira biliyan 3.08, mallakin kananan hukumomin jahar Kano. Wani mutumi mai suna Mustapha Danjuma and Co ne ya kawo da karar Kwankwaso a madadin Abubakar Maisha’ani da Algahji Najumai Kobo.

“Mustapha Danjuma and Co, yana tuhumar Kwankwaso da cewa ya karbi gudunmuwar naira miliyan 70 daga kowacce karamar hukuma cikin kananan hukumomin jahar Kano guda 44 domin gudanar da yakin neman shugaban kasa a shekarar 2015, a jimlace naira biliyan 3.08 kenan.

“Shi kuma Wamakko zamu gayyaceshi ne a domin amsa tambayoyi a kan tuhumarsa da ake yi da satar zunzurutun kudi wuri na gugan wuri har naira biliyan 15.” Inji kaakaki Wilson.

A yanzu dai za’a jira domin ganin yadda zata kaya tsakanin hukumar EFCC da wadannan tsofaffin gwamnoni a game da wannan bincike da take musu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel