Riko da addini, ladabi da biyayya da sauran fa'idodin auren Mace 'yar kabilar Ibo ko Yarbawa

Riko da addini, ladabi da biyayya da sauran fa'idodin auren Mace 'yar kabilar Ibo ko Yarbawa

Babu shakka kabilu daban daban a fadin duniya sun yi wa so kuma kauna fahimta mabanbanta juna, sai dai duk ta karkare sakamakon karshe na duk wata sahihiyar soyayya da ta kullu a tsakanin mace da namiji shi ne aure.

A yayin da zabin ma'abociyar zama ta gari ya zamto daya daga manyan rukunan da ya kamata namiji ya duba gabanin aure kamar yadda addini ya shar'anta, babu shakka mutane da dama su kan tafka kura-kurai a bisa rashin sani ko kuma sa'ilin da ciwon so ya rufe masu idanu.

Aure dai wani mayafi ne da gabanin namiji ko mace ya yafa, akwai bukatar yi wa kai karatun ta nutsu wajen zaben na gari domin samun kwanciyar hankali bayan an zama daya.

Duk da cewa zo mu zauna na tafiya hannu da hannu da zo mu saba, sanadiyar yadda babu ta yadda za a yi mutane biyu su zauna ba tare da daya ya sabawa daya ba, wannan shi masu hangen nesa ke yi wa lakabi da gishirin zaman duniya.

KARANTA KUMA: An kama manyan 'yan ta'adda 5 masu yiwa Boko Haram hidima a Borno

A wani rahoto dangane da zabin macen da namiji zai aura da muka kalato a jaridar The Nation, ya bayyana fa'idodin auren macen da ta fito daga manyan kabilu biyu na yankin Kudancin Najeriya na Ibo a Kudu maso Gabas da kuma Yarbawa a Kudu maso Yamma.

Ga dai fa'idar auren mace 'yar kabilar Ibo

1. Kyawun sura da halitta.

2. Kololuwar iya sanwa wato girki mai dan karen dadi. An yi itifakin cewa babu matan da suka fi na Ibo iya girki mai dadi a Najeriya.

3. 'Kaunar 'ya'ya da ladabtar da su akan kyawawan dabi'u

4. Riko da al'ada.

5. Yawan ziyarar 'yan uwa.

6. Riko da addini.

7. Rashin cin amana da keta haddin aure.

Ga kuma fa'idodin auren mace 'yar kabilar Yarbawa

1. Ladabi da biyayya. An yi itifakin cewa babu matan da suka fi na Yarbawa ladabi da biyayya a Najeriya.

2. Jajircewa wajen neman na kai.

3. Ilimi da kaifin basira.

4. Kyawun jiki da rashin tsufa da wuri.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel