Kananun ma'aikatan gwamnatin tarayya sun soma karbar mafi karancin albashi na N30,000 - Ngige

Kananun ma'aikatan gwamnatin tarayya sun soma karbar mafi karancin albashi na N30,000 - Ngige

- Ma'aikatan gwamnatin tarayya sun soma karbar mafi karancin albashi na naira 30,000 inji Chris Ngige

- A cewar ministan, an fara kaddamar da wannan kudiri ne kadai a kan kananan ma'aikata daga matsayi na farko zuwa na shida

- Ministan ya ce manyan ma'aikata su sha kurumin su gabanin sabon sabon tsarin ya kawo gare su

Ministan kwadago na Najeriya, Dakta Chris Ngige, ya yi farin albishir da cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fara biyan kananan ma'aikatan gwamnatin tarayya mafi karancin albashin na naira dubu talatin.

Ministan wanda ya bayyana hakan a birnin Enugu, ya yi watsi da ikirarin kungiyar kwadago ta Najeriya wadda ta ce gwamnatin tarayya ba ta da niyyar fara biyan mafi karancin albashin ma'aikata kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Dakta Ngige ya ce kaddamar da wannan sabon tsari na fara biyan mafi karancin albashin dukkanin ma'aikatan babban kalubale ne da ba zai tabbata ba lokaci guda cikin gaggawa face daki-daki.

Ya ce ya zuwa yanzu wannan sabon tsari ya fara tasiri a kan kananan ma'aikatan gwamnatin tarayya daga kan mataki na daya zuwa na shida. An sauya mafi karancin albashin kananan ma'aikatan daga kan N18,000 zuwa N30,000.

KARANTA KUMA: Taron Majalisar Dinkin Duniya: Buhari ya isa kasar Amurka

Sai dai ministan ya ce babu shakka karin mafi karancin albashin ma'aikatan ba zai takaita kadai a kan kananan ma'aikata ba domin kuwa zai yadu har zuwa ga manya, lamarin da ya ce ba zai yiwu kananan ma'aikata da manya su rinka daukan albashi kai daya.

Ana iya tuna cewa, tun a watan Afrilun da ya gabata ne shugaban kasa Buhari ya rattaba hannu kan kudin sabon mafi karancin albashin ma'aikata a Najeriya, inda kuma a watan Yulin da ya gabata shugaban kasar ya amince a fara biyan sabon albashin na N30,000 ga ma'aikata masu daukan kasa da hakan.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel