Yadda aka kama gwamnan Kebbi, Abubakar Bagudu a kasar Amurka

Yadda aka kama gwamnan Kebbi, Abubakar Bagudu a kasar Amurka

Tun kafin a zabe shi a matsayin gwamnan jihar Kebbi, lauyoyi a kasar Amurka da Ingila sun ce Abubakar Bagudi na jihar Kebbi na daya daga cikin wadanda ke tallafawa tsohon shugaban mulkin soji Sani Abacha wurin boye kudaden sata.

Kafin rasuwarsa a 1998, tsohon shugban Sani Abacha ya saci kimanin dala biliyan 2.2 daga asusun kasar.

Premium Times ta ruwaito cewa hujojjin da aka gabatarwa kotu ya nuna cewa Bagudu ne jigo wurin karkatar da kudaden al'umma a madadin Abacha.

Binciken da lauyoyin suka gudanar da hadin kan wasu 'yan uwan Bagudu, wasu manyan gwamnatin Abacha da Mohammed (Babban dan Abacha), sunyi ikirarin cewa gwamnan ya yi amfani da wasu kamfanoni wurin karkatar da miliyoyin daloli daga asusun gwamnati zuwa wasu asusun ajiya na kasashen waje mallakarsa da Abacha.

Karkatar da kudaden da Bagudu ya yi wa Abacha suna kunshe cikin takaradan karar da kaa shigar a Amurka da Bailiwick da ke Jersey wata kamfanin kasar Ingila da ke Channels Islands.

Duk da cewa masu bincike sunyi imanin cewa Bagudu yana da masu tallafa masa wurin karkatar da kudade a wurare da dama, yana bukatar taimakon matarsa da yayansa Ibrahim. Kuma ya fi son ajiye kudin a kasar Jersey.

A 2003, shekaru biyar bayan rasuwar Abacha, an gano cewa tabbas ya saci kudin gwamnati saboda an gano wasu kudaden a Jersey. Mahukuntan kasar sun nemi taimakon Amurka domin kamo Bagudu wanda ya lokacin yana zaune a jihar Texas na Amurka.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Dauke wutan lantarki ya hana kotun zaben gwamna yanke hukunci

Daga bisani an kama Bagudu kuma aka tsare shi na tsawon watanni shida inda ake jirar kammala shirin aikewa da shi kasar Jersey domin ya amsa tambayoyi kan kudaden da aka gano a asusun kamfanin Doraville Properties Corp. da ke karkashin kulawar Bagudu da Mohammed.

Amma kafin a kai ga mika shi ga jami'an tsaro a Jersey, Mista Bagudu ya yi yarjejeniyar gagagwa da mahukuntan kasar Amurka da Jersey inda ya mayar da "fiye da kadarorin da kudinsu ya kai dala miliyan 163 da ake zargin an kartatar zuwa Najeriya domin kasar Jersey ta janye bukatar gurfanar da shi kuma a dawo da shi Najeriya," kamar yadda wata takardan kotu ta Premium Times ta samu ya nuna.

Bayan yarjejeniyar da aka kulla da kasar Jersey da Amurka, An saki Bagudu kan cewa zai dawo Najeriya ya fuskanci shari'a. An aike wa alkalin alkalan Najeriya dukkan hujojjin da aka tattara kan Bagudu don ya taimaka musu wurin gurfanar da shi a kotu.

Sai dai tun dawowarsa, ba a gurfanar da shi a gaban kotu ba kan rawar da ya taka na satar kudaden da Abacha ya yi a maimakon haka an tantance shi shiga takara har sau uku na farko a matsayin sanata sai kuma sauran biyun a matsayin gwamna inda duk ya lashe zabukkan.

Duk yunkurin da aka yi na tuntubar Bagudu da Minstan Shari'a, Abubakar Malami kan batun shari'ar da takardun da Amurka ta aike masa amma hakan ya ci tura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel