Tashin hankali: Likitoci sun ciro cokula guda 20 a cikin wani mutumi marar lafiya

Tashin hankali: Likitoci sun ciro cokula guda 20 a cikin wani mutumi marar lafiya

- Wata tiyata da aka yiwa wani matashin saurayi dan shekara 20 a duniya an ciro abubuwa sama da talatin a cikin shi, ciki kuwa hadda cokula guda ashirin da hudu

- Wannan lamari dai ya faru a kasar Egypt ne a babban birnin Cairo, inda aka garzaya da matashin zuwa asibiti bayan ya fara korafin cikin shi nayi masa ciwo

- Likitan da ya yiwa saurayin tiyatar ya bayyana cewa matashin ya hadiye wadannan abubuwa ne tsawon watanni shida da suka gabata

Wani abun mamaki da ya faru a birnin Cairo na kasar Egypt, yayin da aka kai wani matashin saurayi asibiti bayan ya fara korafi cewa cikin shi na yi masa ciwo. Abubuwan da likitocin suka samo a cikin shi sun bawa kowa mamaki.

Shugaban likitocin Dr. Amjad Fouad ya bayyana cewa binciken da suka yi sun gano cokula da wasu abubuwa a cikin marar lafiyan.

Matashin mai shekaru 20 ya samu matsalar tabin hankali. Bayan likitocin sun yi masa tiyata sai suka samu cokula guda ashirin, cokula masu yatsu guda hudu, zoben zinare, sarka da dan kunne da dai sauran abubuwa masu tarin yawa a cikin nashi.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama mutane 15 da suke da hannu wajen yunkurin kashe matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Yanzu haka dai an cire duka abubuwan a cikin marar lafiyan, kuma ya samu sauki. Yanzu dai tambayar da ake yi ita ce, ya aka yi duka wadannan abubuwa suka shiga cikin shi? A cewar likitan da yayi wannan tiyata, yace matashin ya hadiye wadannan abubuwan na tsawon watanni shida, yana kuma yawo da su a cikin shi na tsawon wannan lokacin.

Haka ita ma mahaifiyar matashin ta bayyana cewa ita ma tayi mamaki yadda taga wasu abubuwa suna bacewa a wajen dafa abincinta, amma ba ta taba kawowa shine yake hadiyewa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel