Mata 'yan siyasa sun bayyana yadda maza ke neman yin lalata da su kafin su zabe su
Dokar aiki ta 'Nigerian Labour Act' bai tanadi wani hukunci ba ga laifin cin zarafin mata ta hanyar neman lalata da su ba a wurin aiki. Galibi ma ba a cika shigar da kara idan irin hakan ya faru ba. Wannan lamari bai tsaya da kananan ma'aikata mata ba har ma manyan mata 'yan siyasa abin ya shafe su.
Mutane za suyi tunanin lamarin ba zai shafi manyan mata 'yan siyasa ba amma batun ba haka ya ke ba. Okunola Abiola mai shekaru 27 ta yi takarar kujerar majalisa a jihar Legas kuma ta fuskanci matsalar kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Ta ce, "Wasu jiga-jigan mazauna Ikeja sun nemi in yi lalata da su idan har ina son lashe zaben. Mazu zabe ma sunyi alkawarin jefa min kuri'a muddin zan amince inyi soyaya da su ko lalata da su."
"Sau da yawa, an ci zarafi na; Ta kalaman baki ko kuma a aikace kuma wannan na daya daga cikin abinda ya janyo min koma baya."
Abiola tayi takarar kujerar majalisa na wakilcin mazabar Ikeja ne karkashin jam'iyyar Alliance for Social Democrats (ASD) na jihar Legas.
DUBA WANNAN: Da duminsa: Kotu ta sake tabbatarwa wani gwamnan PDP nasara
Jihar Legas itace jiha ta farko a Najeriya da ta kafa doka da za ta hukunta wanda aka samu da laifin cin zarafi ta hanyar lalata a karkashin sashi na 262(i) na dokar jihar ta shekarar 2011.
Dokar ta tanadi hukuncin shekaru uku a gidan gyaran hali ga duk wanda aka samu da laifin cin zarafin wani ta hanyar lalata.
Alkalluman da cibiyar demokradiyya da cigaban kasa (CDD) ta wallafa ya nuna cewa 'yan takara 11.36 cikin 100 ne kawai mata a zaben da ya gabata.
Matsalolin da aka fuskanta a zaben sun hada da tayar da rikici, yi wa masu zabe da 'yan takara barazana tare da cin zarafin mata ta hanyar neman yin lalata da su. CDD ta ce akwai bukatar yin bincike kan lamarin a kuma hukunta wadanda aka samu da laifi domin ya zama darasi ga wasu.
Sylvanus Okeoma wacce tayi takarar majalisar jihar a mazabar Agwu North a jihar Enugu a karkashin jam'iyyar African Democratic Party ta ce, "Na fuskanci cin zarafi na neman lalata dani kuma an kai wa jami'ai na hari."
Ta bayar da shawarar a yi doka da zai rika hukunta masu aikata laifin domin duk lokacin da tayi yunkurin tayar da zancen a kan shashantar da batun ne.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng