Tirkashi: Allah yana nan a madakata, shi zai bi mini hakkina ranar gobe kiyama - Sakon Atiku ga Buhari

Tirkashi: Allah yana nan a madakata, shi zai bi mini hakkina ranar gobe kiyama - Sakon Atiku ga Buhari

- Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP yayi wata muhimmiyar magana akan shari'ar da kotu ta yi

- Ya bayyana cewa Allah yana nan yana jiran kowa a madakata, kuma shine zai bi mashi hakkin shi a ranar gobe kiyama

- Tsohon mataimakin shugaban kasar dai ya kai karar shugaban kasa Muhammadu Buhari kotu akan cewa yayi magudin zabe a zaben shugaban kasa da aka yi a wannan shekarar

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a martanin da ya mayar a ranar 11 ga watan Satumbar nan, bayan anyi watsi da kararshi da ya kai gaban kotun sauraron karar akan shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayi wata magana akan yadda Allah zai bi mishi hakkin shi a ranar gobe kiyama ga dukkanin mutanen da suke da hannu a wannan shari'ar zabe.

Atiku wanda yake kokarin ganin ya kwato hakkin shi daga wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya bayyanawa kotun sauraron zabe cewa yana da kuri'u masu yawa fiye dana shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Hakan ya sanya yace sai inda karfin shi ya kare wajen neman hakkin shi akan wannan magudin zabe da aka yi masa.

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Wata budurwa tayi ridda ta koma addinin Kiristanci

Tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda a yanzu haka yake kasar Dubai hutu ya saki wata sanarwa a jiya Juma'a ga masoyansa, inda yake cewa kotun koli za ta yi hukuncin da ya kamata a wannan shari'a ta shi.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce: "Ina bukatar 'yan Najeriya su cigaba da nuna goyon bayansu akan shari'ar da za ayi, ko da kuwa babu abinda muka isa muyi akan shari'ar, mu yarda cewa zamu yinasara. Kada mu taba kokwanton hakan ba zai yiwu ba," in ji tsohon mataimakin shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel