Kowa yaki jin bari zai ji ho-ho: Na yi dana sanin auren 'Slay Queen' a rayuwata - Wani mutumi ya koka

Kowa yaki jin bari zai ji ho-ho: Na yi dana sanin auren 'Slay Queen' a rayuwata - Wani mutumi ya koka

- Wani magidanci ya koka da halin da matar shi ta sanya shi a ciki, inda ya bayyana cewa rabuwa zai yi da ita dole

- Ya ce lokacin da yake nemanta ta nuna masa cewa ita macen arziki ce, amma kuma wani abun mamaki bayan ya aureta sai ta canja halayenta

- Mutumin ya gargadi samari masu son auren mata 'yan bana bakwai da su lura da kyau yawancin su ba na arziki bane

Wani mutumi ya nuna bacin rai da bakin ciki bayan shafe watanni biyar da yin sabon auren shi. Mutumin yaje shafin sada zumunta na zamani ya gargadi maza da suke tunanin auren mata 'yan bana bakwai wato 'Slay Queens'.

A cewar mutumin, ya auri matat shi wacce take 'yar bana bakwai 'Slay Queen', wacce a lokacin da yake kokarin aurenta ta nuna mishi tabbas cewa ita macen arziki ce, sai dai kuma daga baya ya sabanin haka bayan auren su.

Mutumin ya bayyana cewa ya gaji da zama da ita dan haka ya yanke shawarar rabuwa da ita.

KU KARANTA: Tirkashi: Limami ya bayyana yadda wata karuwa da ya hadu da ita tayi kokarin yi masa fyade

"Yanzu muna sabon wata, bazan iya cigaba da zama haka ba wallahi. Na auri wata yarinya wacce ta nuna mini cewa ita macen arziki ce a lokacin da muna soyayya tsawon shekara daya banga aibun ta ba. Yanzu haka watan mu biyar kacal da yin aure amma har na gaji da zama da ita.

"Yawancin mata mayaudara ne, ta yaudare ni saboda na hadu da ita a coci. Yanzu kuma zanyi mata sakin da baza ta taba mantawa da shi ba. Ba zan iya cigaba da zama da ita ba.

"'Yan uwa ku lura da kyau ba duka matan da kuke haduwa da su a wajen ibada bane na gari, ku fara yin addu'a Allah ya baku macen kirki ba dole sai a wajen ibada ba," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel