Ke duniya! Budurwa ta yi garkuwa da kaninta, ta nemi a biya naira miliyan 6 a Adamawa

Ke duniya! Budurwa ta yi garkuwa da kaninta, ta nemi a biya naira miliyan 6 a Adamawa

Jami’an Yansanda masu yaki da fashi da makami, SARS sun samu nasarar cafke wata budurwa yar shekara 18 mai suna Hadiza Babayo da laifin satar kaninta dan shekara 5, tare da yin garkuwa da shi, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Hadiza Babayo wanda yar asalin karamar hukumar Lafiya Lamurde na jahar Adamawa ta hada baki da wani matashi mai suna Bala Shuaibu, inda suka sace diyar kawunta daga makaranta, suka yi garkuwa da ita suna neman kudin fansa naira miliyan 6.

KU KARANTA: Ilimi gishirin zaman duniya: Tsohuwa yar shekara 76 ta kammala karatun digiri a Katsina

Ke duniya! Budurwa ta yi garkuwa da kaninta, ta nemi a biya naira miliyan 6 a Adamawa
Hadiza
Asali: Facebook

Da yake bayyanasu ga manema labaru, kaakakin rundunar Yansandan jahar Gombe, SP Obed Mary Malum ta bayyana cewa sun kama Hadiza ne bayan ta boye yarinyar a wani Otal dake yankin Nayi-Nawa na jahar Gombe.

Amma bayan gudanar da cikakken bincike, jami’an Yansandan SARS sun samu bayanai game da inda Hadiza take, a haka suka mamaye Otal din, suka kamata da abokin aikin nata ba tare da biyan ko anini ba, kuma tuni ta amsa laifinta.

Daga karshe kaakaki Mary ta bayyana cewa zasu gurfanar da Hadiza da Shuaibu gaban kuliya manta sabo da zarar sun kammala gudanar da bincike.

A wani labari kuma, wata mata yar shekara 22, Harela Uba ta shiga hannun Yansandan jahar Neja bayan ta shayar da jaririn kishiyarta wanda bai wuce kwanaki 3 a duniya ba kacal gubar fiya fiya, inda take ya zamto matacce.

Harela ta aikata wannan ta’asa ne a ranar 14 ga watan Satumba a gidansu dake kauyen Shakodna cikin karamar hukumar Shiroro na jahar Neja, kuma mijinta, Uba Saidu ne ya kai karar matarsa tasa da kansa ga Yansanda.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel