Tashin hankali sai kace zomo: An gano wani mutumi da ya haifi 'ya'ya 1,300 a duniya

Tashin hankali sai kace zomo: An gano wani mutumi da ya haifi 'ya'ya 1,300 a duniya

Wani bincike da aka yi na sirri, wanda wasu mutane dake garin Tennessee suka bayar ayi, ya bayyana wani mutumi mai shekaru 87 ya haifi 'ya'ya 1,300 a duniya

Binciken da likitoci suka yi ya bayyana dubunnan misalai na DNA na tsawon shekaru 15, inda hakan ya nuna cewa tabbas wannan mutumi yana da 'ya'ya sama da dubu daya a cikin wannan yankin na su.

"Bana jin kunyar komai, a lokacin da nayi zamani na saboda ina da kudi, hakan yasa 'yammata suka dinga rububi na," in ji shi. "A lokacin duka idonsu ya rufe, kowacce so take na dinga kwanciya da ita, ni wanene da zan samu dama irin wannan nayi wasa da ita," in ji mutumin ya kara bayani.

Mutumin da aka dauka ya gabatar da wannan bincike shi ma yayi magana kamar haka:

"Lamarin ya samo asali ne lokacin da wasu mutane guda biyu wadanda duka basu san juna ba suka dauke ni aiki akan na nemo musu ainahin mahaifinsu. Nayi mamaki matuka bayan na gano cewa duka su biyun 'ya'yan mutum daya ne. A wannan lokacin ne abin ya fara, hakan ya saka na dauki aikin da muhimmanci, duk lokacin da nake bana komai sai na cigaba da bincike akan wannan mutumi, na samo DNA na mutane masu dumbin yawa wadanda suke da alaka da mutumin nan a wadannan 'yan shekarun," in ji shi.

KU KARANTA: Tirkashi: 'Yan sanda zasu kama duk wani matashi da suka gani yana rike da wayar iPhone 11 daga nan zuwa Disamba

Mutumin ya cigaba da cewa 'ya'yan mutumin sun nuna ba za su kai karar shi wajen kotu ba.

"Yawancin mutanen dana gano cewa 'ya'yan shine ba su so zancen ya fita," in ji likitan. "Idan mutane suka san gaskiyar lamarin za a samu babbar matsala domin hakan zai iya kawo karshen zaman auren ma'aurata da yawa, kuma ni ba nayi binciken saboda haka bane. Kawai dai na san mutane da yawa sunji dadin gaskiyar abinda na binciko, kuma ba su nuna bacin rai akan tsohon ba."

Duk binciken da Sid Roy yayi akan wannan tsoho ya nuna masa cewa yana da 'ya'ya 1,300, ya bayyana cewa akwai yiwuwar a samu wasu 'ya'yan kuma idan ya cigaba da binciken na shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel