Ilimi gishirin zaman duniya: Tsohuwa yar shekara 76 ta kammala karatun digiri a Katsina

Ilimi gishirin zaman duniya: Tsohuwa yar shekara 76 ta kammala karatun digiri a Katsina

Tabbas girma ko shekaru basa hana neman ilimi, wannan kuwa ya tabbata kamar yadda dattijuwa, Hajiya Fatima Kurfi ta tabbatar bayan ta samu shaidar kammala karatun digiri na farko yayin da take da shekaru 76 a duniya.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Abubakar Kabir Ingawa ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda yace Hajiya Fatima ta yi karatun digiri ne a jami’ar Al-Qalam na jahar Katsina inda ta karanci fannin karatun addinin Musulunci, B.Sc Islamic Studies.

KU KARANTA: Mugunta ruwan fakko: Uwargida ta kashe jaririn kishiyarta da fiya fiya

Ilimi gishirin zaman duniya: Tsohuwa yar shekara 76 ta kammala karatun digiri a Katsina
Hajiya Fatima
Asali: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Hajiya Fatima ta kammala digirin ne a shekarar 2009, amma sai ya zaman ba yi bikin yaye daliban jami’ar ba har sai shekarar 2016. Hajiya Fatima bata samu daman yin karatu ba yayin da take budurwa, amma ta fara koyon rubutu da karatu bayan ta yi auri, inda suka koma kasar Ingila tare da mijinta.

Bayan dawowarsu daga kasar Ingila ne ta koma karatu a kwalejin horas da malaman Larabci inda ta kammala karatun sakandari, a wannan lokaci kuma ajinta daya da guda cikin jikokinta, daga bisani kuma ta samu difloma a kwalejin larabci ta Danfodio dake garin Katsina.

Hajiya Fatima bata nuna gajiyawa ba inda ta kara neman gurbin cigaba da karatu a jami’ar Al-Qalam a shekarar 2005, a yanzu haka Hajiya Fatima tana da makaranta mai zaman kanta, kuma tana da kungiya mai zaman kanta dake baiwa mata kwarin gwiwar neman ilimi.

A yanzu haka Hajiya Fatima tana cigaba da karance karance da kuma gudanar da bincike daban daban, Hajiya Fatima tana aurenan Dakta Ahmadu Kurfi, wanda ya zama babban sakatare a ma’aikatar gwamnatin tarayya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel