CBN ta ware naira biliyan 30 domin habbaka noman kwakwan manja a Najeriya

CBN ta ware naira biliyan 30 domin habbaka noman kwakwan manja a Najeriya

Babban bankin Najeriya, CBN ta bayyana cewa ta ware kimanin kudi naira biliyan 30 domin habbaka noma kwakwan manja a Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito gwamnan bankin, Godwin Emefiele yana fadi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Emefiele ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da wasu gwamnoni a babban birnin tarayya Abuja ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba, inda yace sun raba kudaden ne ga wasu kamfanoni guda 6 ta hannun bankuna.

KU KARANTA: Gwamnatin Sakkwato ta biya ma daliban jahar zunzurutun kudi na WAEC da NECO

Daga cikin kamfanonin da suka samu wannan tallafi domin fadada noman kwakwan manja akwai PZ Wimar, Biase Oile company ltd, Eyop, Okomu Oil company, Presco oil company da kuma SIAT ltd, ya kara da cewa suna jiran kamfanin Ada Palm na jahar Imo ta ma ta mika kokon bararta.

Emefele ya bayyana cewa Najeriya na bukatar tan miliyan 2.5 na manja a shekara, amma tan miliyan 1.25 kadai ake iya samarwa a kasa, wanda hakan ya samar da gibin tan miliyan 1.25 da ake bukatar rufeshi a cikin gida, saboda a yanzu sai an shigo da manjan daga kasashen waje ake cike gibin.

“Muddin muna son cike wannan gibin sai mun noma sabbin hektocin gona 312,500 a karkashin tsarin noman zamani tare da sa ran samun tan 4 a kowanne hekta, fatanmu shine noma hekta miliyna 1.4 a cikin shekaru 3.

“Hakan tasa muka gana da gwamnonin jahohin Najeriya 14 inda kowanne gwamna ya yi alkawarin samar da hekta 100,000 na gona a jaharsa, a yanzu haka muna da hekta 904,624 wanda jahohi zasu bayar ga masu zuba jari, kuma mun aika musu masu zuba jarin domin a fara tsarin mika musu gonakan.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng