Gwamnatin Sakkwato ta biya ma daliban jahar zunzurutun kudi na WAEC da NECO

Gwamnatin Sakkwato ta biya ma daliban jahar zunzurutun kudi na WAEC da NECO

Gwamnatin jahar Sakkwato ta sanar da biyan kimanin naira miliyan 300 don biya ma daliban jahar kudin jarabawar kammala sakandari na WAEC da NECO na shekarar 2018/2019 wanda hukumomin jarabawar ke binta bashi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kaakakin ma’aikatan ilimi na jahar, Nura Bello Maikwanci ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba a garin Sakkwato inda yace gwamnati ta biya kudaden ne domin a sako sakamakon jarabawar daliban.

KU KARANTA: Tattalin arziki: Dangote ya jinjina ma Buhari game da zabo kwararrun mashawarta

Don haka Maikwanci ya shawarci daliban jahar da iyayensu dasu kara hakuri saboda gwamnati na daukan duk matakan da suka kamata don tabbatar da an sako sakamakon jarabawar yayansu cikin lokaci.

“An biya kudaden ne domin daliban da suka zana jarabawar da hukumar WAEC da NECO suke shiryawa, kuma muna sa ran da wannan cigaba da aka samu, hukumomin za su saki sakamakon jarabawar nan bada jimawa ba.” Inji shi.

A wani labarin kuma, matasan Najeriya a karkashin hukumar matasan Najeriya ta kasa, National Youth Council of Nigeria sun tashi tsaye domin yaki da miyagun aikin luwadi da madigo a Najeriya ta hanyar gudanar da zanga zangar kyamatar hayalayen biyu.

Mataimakin shugaban NYCN, reshen yankin Arewa ta tsakiya, Akoshile Mukhtar ne ya jagoranci wannan zanga zanga da suka gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 18 ga watan Satumba.

Akoshile yace suna yaki da kungiyoyin luwadi, madigo, da ire irensu saboda munanan dabi’u ne a tsakanin al’umma, don haka suke kokarin kawar dasu daga cikin al’umma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel