'Yan sanda sun rufe ofishin O'Pay a Kano
'Yan sandan Najeriya reshen jihar Kano sun rufe ofishin da 'yan adaidaita sahu ke biyan kudi ta kafar Intanet mai suna OPay.
An rufe ofishin ne yayin wata sumame da 'yan sanda suka yi a Kano kan rashin bin dokokin gwamnati da kamfanin baya yi.
The Nation ta ruwaito cewa jami'an tsaro dauke da bindigu sun isa ofishin kamfanin da ke Lodge road a Kano misalin karfe 11 na safe a ranar Alhamis.
'Yan sanda sun umurci dukkan ma'aikatan kamfanin da masu adaidaita sahu da ke wurin su fice inda su kayi barazanar kama dukkan wanda bai yi biyaya ga umurnin ba.
DUBA WANNAN: An bayyana yadda 'yan bindiga suka bi wani basaraken arewa har gida suka kashe shi
Wani wanda abin ya faru a idonsa ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa masu adaidaita sahun suna shirin biyan kudin cinikin su da daren Laraba ne 'yan sandan suka iso suka tarwatsa su.
Mai magana da yawun 'yan sanda na jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce gwamnatin jihar Kano ce ta bawa rundunar umurnin rufe wurin.
Haruna ya ce kamfanin na Opay ya saba wasu dokoki da gwamnatin jihar ta kafa masa muddin yana son yin aiki a jihar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng