Kiwon lafiya: Dabaru 5 da za’a iya bi don magance ciwon ciki cikin sauki

Kiwon lafiya: Dabaru 5 da za’a iya bi don magance ciwon ciki cikin sauki

Sanannen abu ne cewa ciwon ciki wani ciwo ne da yake yawan samun mutane da dama a cikin al’umma, sai dai yawancin abinda ke janyo ciwon ciki ba wani babban lamari bane, don haka kana iya maganceshi cikin sauki ta hanyar amfani da wasu dabaru kamar haka:

- Ruwan Kaal

Ruwan Kaal wani ruwa ne mai tsami sosai wanda ake sayar da shi a cikin kwalba, ana iya shan cokali guda na ruwan don warware ciwon ciki, idan kuma ba za ka iya ba saboda karfin ruwan, kana iya sirka shi da ruwan ko zuma. Ana kuma iya shan shi a matsayin kandagarki.

KU KARANTA: Tattalin arziki: Dangote ya jinjina ma Buhari game da zabo kwararrun mashawarta

- Citta

Ga wadanda suka sani, ana iya amfani da citta wajen magance kasala, haka zalika citta na taimakawa wajen kawar da ciwon ciki sakamakon yana warware kumburin ciki, ana iya tauna cittar a danyenta ko kuma a jikata a sha.

- Furen Chamomile

Ita ma Furen Chamomile ana iya amfani da ita wajen magance ciwon ciki musamman idan aka jikata da ruwan zafi, sai a sha shi a kamar ruwan Tea, ita Chamomile tana saukar da kumburin ciki tare da warware bangon cikin mutum, ta haka take saukaka zafin da ake ji a cikin ciki.

- Hadin shikafa, ayaba, tufa da burodi

Wannan ma wani hadi ne da ake hada shinkafa, ayaba, nikakken tufa da kuma gasashshen burodi wanda aka ci shi za a yi bankwana da cutar ciwon ciki nan take. Haka zalika hadin na magance zawo da kasala.

- Gasa ciki

Duk mai ciwon ciki zai iya samun kwalba mai dumi, sai ya kanga shi a cikinsa, a hankali cikin sauki zai warware ma mutum ciwon cikin da duk wanda murdewar ciki da yake fama dashi. Sai dai a kula, kada a bari kwalbar ta dade a cikin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel