Kai jama'a: Wani mutumi ya yiwa matarshi saki uku saboda gajiya da yayi da biyan kudin kitso

Kai jama'a: Wani mutumi ya yiwa matarshi saki uku saboda gajiya da yayi da biyan kudin kitso

- Wata taga ta kanta, bayan mijin da ta jima tana zaune da shi yayi mata saki uku kawai saboda tana tambayar shi kudin kitso

- Mijin ya bayyana cewa shekarar su bakwai suna tare da matar tashi, kuma yana mutukar sonta, amma kuma ya ce sai dai tayi hakuri mai faruwa ta faru

- Inda ya bayyana cewa babu yadda za ayi yaje yayi aiki ya wahala kawai yazo ya kawo mata kudin taje ta sanya gashin doki a kanta

Wani mutumi dan birnin Atlanta dake kasar Amurka ya saki matarsa wacce suke zaune lami lafiya na tsawon shekara bakwai, saboda abinda ya fada na cewa ya gaji da biya mata kudin kitso, kamar dai yadda takardun kotu suka bayyana.

Mutumin mai suna Jonathan Rhames ya bayyana cewa yana mutukar son matarsa tamkar ba zai iya rayuwa babu ita ba, amma kuma shi bai ga wani dalili da zai saka ya dinga fita yana wahala a wajen aiki ba, sannan a karshe ya dawo ya kawo mata kudin taje ta sanya gashi, gashin ma kuma na doki.

Mutumin ya ce: "Zai fi mini sauki mu sayi dokin sukutum in yaso sai mu dinga yakar gashin idan ya girma."

KU KARANTA: Allah ya shirya mana zuri'a: Yaro dan shekara 11 ya shiga kungiyar 'yan ta'adda bayan rabuwar iyayenshi

Shekaru biyar da suka wuce dai farashin gashi na sanyawa a kai yayi tashin gauron zabi inda ya kara kudi sosai a kasuwa.

Wannan labari dai an wallafa shi a shafukan sadarwa na zamani, inda mutane kowa ke tofa albarkacin bakinsa, wasu na cewa bai kamata dama matar ta dorawa mijin alhakin komai ba, kamata yayi su dinga raba wahalar ita ma ta fita taje ta nemo kamar yadda yake fita yana nema.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel