Allah ya shirya mana zuri'a: Yaro dan shekara 11 ya shiga kungiyar 'yan ta'adda bayan rabuwar iyayenshi

Allah ya shirya mana zuri'a: Yaro dan shekara 11 ya shiga kungiyar 'yan ta'adda bayan rabuwar iyayenshi

- A cikin mutane 71 da hukumar 'yan sandan jihar Legas ta kama an samu wani yaro mai shekaru 11 a cikinsu

- Yaron ya bayyana cewa bayan rabuwar iyayen shi ne ya yanke hukunci dawowa Legas da zama, inda ya zama dan aiken 'yan ta'addar

- Yace a hankali bayan sun fara aiken shi sai suka fara bashi kwaya yana sha har ma yazo ya saba

Wani yaro dan shekara 11 yana daya daga cikin 'yan sara sukan da jami'an hukumar 'yan sanda na jihar Legas suka kama jiya Laraba a yankin Oshodi, ya bayyana cewa ya shiga wannan kungiya ta 'yan ta'adda ne saboda mahaifin shi da mahaifiyarsa sun rabu.

Yaron yana daya daga cikin mutane 71 da aka kama a kasan gadar Oshodi a wani sumame da rundunar 'yan sanda ta kai yankin, amma daga baya an kai shi bangaren bayar da tarbiyya domin a lura da shi.

Yaron ya ce ya zo jihar Legas ne daga daya daga cikin jihohin da suke makwabtaka da ita, bayan iyayen shi sun rabu, kuma yayi kokarin daidaita su lamarin yaci tura.

KU KARANTA: Tirkashi: Malami yaga ta kanshi yayin da ya sha maganin karin karfin maza domin ya burge karuwar shi

Ya bayyanawa jaridar Vanguard cewa yana kwana a kasan gadar ne inda daga baya ya zama dan aiken 'yan ta'addar. "A hankali aka fara bani kwaya ina sha," in ji yaron.

Shugaban rundunar 'yan sanda CSP Olayinka Egbeyemi, wanda ya jagoranci kai sumamen, ya bayyana cewa wannan sumame da suka kai yana daya daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi domin ganin ta kawo karshen ta'addanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel