Gwamnan jahar Kwara ya bayyana dalilin da yasa ya nada yar shekara 26 kwamishina

Gwamnan jahar Kwara ya bayyana dalilin da yasa ya nada yar shekara 26 kwamishina

Gwamnan jahar Kwara, Abdulrazak Abdulrahman ya bayyana dalilinsa na nada wata budurwa yar shekara 26 wanda a yanzu hake take hidimar bautan kasa NYSC, mukamin kwamishina a gwamnatinsa, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Talata ne aka samu rahoton gwamnan ya sanar da Joana Kolo a matsayin guda daga cikin mutanen da yake muradin nadawa mukamin kwamishina a sabuwar gwamnatinsa.

KU KARANTA: Rusau a Kaduna: Yan kasuwannin Kaduna sun fara yi ma El-Rufai addu’a

Da yake zantawa da manema labaru, mai magana da yawun gwamnan, Rafiu Ajakaye ya bayyana cewa nadin Joana ya yi daidai sakamakon mace ce jajirtacciya, kuma gwamnan ya yi haka ne domin gwaraya masu rike da mukaman iko a jahar, wanda duk maza ne suka mamaye.

“A zaben daya gabata, babu mukamin da mace ta samu nasara, haka zalika duk wadanda aka nada mukamai mata ne. don haka muke kokarin shigar da mata harkar gwamnati, kuma har yanzu babu wanda ya kawo wata mummunar shaida a kan Joana.

“Koda yake ma gwamna a matsayinsa yana da ikon nada duk wanda yaso mukamin kwamishina matukar zai iya gudanar da aikin dake rataye a kansa, amma dama kun san mutane, ko daga jami’ar Havard aka dauko Farfesa wasu sai sun yi magana.” Inji shi.

A wani labarin kuma, yan kasuwan jahar Kaduna sun fara gudanar da addu’o’i na musamman a kan gwamnatin jahar Kaduna sakamakon manufar gwamnan jahar Kaduna na rusa wasu manyan kasuwannin jahar tare da sake ginasu ginin zamani.

Yan kasuwan sun bayyana rashin gamsuwarsu da manufar gwamnatin na zamanantar da kasuwanni, musamman duba da cewa bata basu wani wurin da za su cigaba da gudanar da kasuwancinsu ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel