Fulani makiyaya sun samu nasara a kotu
Kotun daukaka kara dake zaune a Dutse, jihar Jigawa a ranar Talata ta yi watsi da hukuncin kotun shari'ar da ta bada umurinn fitittikanw asu makiyaya daga muhallansu.
Makiyayi, Muhammadu Jingi, mazaunin garin Fagam, karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa ya shigar da kara kotu ta lauyoyinsa, Baffa Alhassan da Hafizu Abubakar.
Lauyoyin biyu sun tsayawa makiyayin da sauran makiyayan da aka kora kyauta a kotu saboda yan uwan juna ne.
Maigarin Fagam, Auwalu Adamu, ne ya fara shigar da kara kotu inda ya ce wa'adin amfani da filin da aka baiwa makiyayi Muhammadu Jingi ya kare kuma ya ki biyan kudin da aka bukace shi. A cewar Premium Times.
A baya, rahoto ya bayyana yadda akayi kokarin fitittikar wasu Fulani makiyaya daga muhallansu bayan sun kwashe kimanin shekaru hamsin a wajen.
Da farko, kotun Shari'a dake zaune a Gwaram ta baiwa maigarin nasara kuma ta umurci makiyayan su fita daga garin Fagam.
Amma a wannan shari'a ta kotun daukaka kara, Alkali Umar Sadiq ya yi watsi da shari'ar inda ya ce kotun Musuluncin ba tada hurumin sauraron irin wannan karar.
Bayan zama kotun, lauyan makiyayan, Hafizu Abubakar, ya ce lallai shari'a ta wanzu kuma an yi adalci.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng