Matar aure da nemi kotu ta raba aurenta saboda mijinta baya sallah

Matar aure da nemi kotu ta raba aurenta saboda mijinta baya sallah

Wata matar aure, Shamsiyya Muhammad a ranar Laraba ta roki kotun Shari'a na II da ke zamansa a Magajin Gari Kaduna ya raba auren ta da mijinta Sani Adamu saboda ya ki yin sallah.

Mai karar, Shamsiyya da ke zaune a Tudun Wada Kaduna ta ce ba za ta iya cigaba da zama da Adamu ba saboda baya kulawa da ita kuma ya na zagin iyayenta da zarar sun samu rashin jituwa.

Shamsiyya ta ce, "An daura mana aure shekaru shida da suka gabata kuma muna da 'ya'ya biyu, ya biya N40,000 a matsayin sadaki na kuma a shirye na ke in mayar masa da kudin domin a raba auren mu kamar yadda addinin musulunci ya koyar."

Wanda aka shigar karar, Adamu wanda shima ke zaune a Tudun Wada Kaduna ya musanta cewa yana zagin iyayenta ya kuma ce yana yin sallah biyar a kowane rana.

DUBA WANNAN: Majalisar Kano ta roki wani muhimmin alfarma daga wurin Ganduje

Adamu ya kuma ce yana kaunar matarsa kuma ya roki kotu ta basu damar su sasanta.

A baya, wani shaida, Malam Sulaiman Sabo, shugaban mahauta na Kaduna ya ce ya yi kokarin yin sulhu tsakanin ma'auratan amma abin ya ci tura.

"Na sha zama tare da su in sulhunta su, a gaba na za suyi alkawarin yafewa juna su zauna lafiya.

"Daga baya kuma sai inji labarai mara dadi game da su a kan lamarin da na sasanta su. Dukkansu makwabta na ne kuma mahaifin Adamu mahaici ne a karkashi na. Nayi iya kokari na amma abin bai yiwu ba," inji Sabo.

Alkalin kotun, Murtala Nasir ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Satumba bayan sauraron bangarorin biyu, ya ce matar da zo da N40,000 na sadakin da ta mijin ya biya a kanta.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa an dage zaman kotun sau hudu domin bawa Malam Sabo daman sasanta su amma matar tana nan kan bakan ta ne neman a raba auren.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel