Yanzu Yanzu: Sojoji da yan sanda sun mamaye ofishin Sahara Reporters a Lagas

Yanzu Yanzu: Sojoji da yan sanda sun mamaye ofishin Sahara Reporters a Lagas

Rahotanni sun kawo cewa jami’an rundunar yan sandan Najeriya da na sojoji sun yi wa ofishin SaharaReporters, wani jaridar yanar gizo, a jihar Lagas kawanya.

An tattaro cewa ma’aikatan gidan jaridar sun isa wajen aiki da safiyar yau Laraba, 18 ga watan Satumba, amma sai aka hana masu shiga ofishin nasu.

A yanzu haka akwai wata motar yan sanda da aka girke a gaban ofishin. An rahoto cewa jami’an tsaro sun isa harabar wajen da misalin karfe 7:00 na safe sannan suka nemi duk wadanda ke ciki da su fito a nan take.

Hakan na zuwa ne kasa da watanni biyu bayan kama Omoyele Sowore, ma’aikacin jaridar, wanda jami’an yan sandan farin kaya suka kama kan zanga-zangar juyin-juya-hali na kasa baki daya da ya shirya.

An guranar dashi a gaban kotu kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Madalla: An kama mutane 3 kan garkuwa da yaran Shugaban karamar hukuma a Katsina

A wani labari na daban, mun ji cewa ‘Dan takarar shugaban kasar jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya a zaben 2019, Obadiah Mailafia, ya bayyana yadda APC ta nemi ya dawo cikin tafiyar jam’iyyar saboda a yafe masa zunubansa.

A Ranar Talata, 17 ga Watan Satumban 2019, Obadiah Mailafia yake cewa jam’iyyar APC mai mulki ta yi kokarin janyo sa a jikin ta da nufin za a yafe masa laifin da bai taba aikatawa a Duniya ba.

A cewarsa, Jiga-jigan APC sun yi tunanin ya na harin shigowa jam’iyyar ne bayan zabe. Mailafia ya yi wannan bayani ne lokacin da ya zanta da Menama labarai a Hedikwatar ADC a Garin Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel