Tirkashi: An kama Aisha Zakari matar da take kiran gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu tana tsorata shi ta wayar salula
- Wata mata da aka jima ana nemanta ruwa ajallo ta shiga hannu, bayan zargin ta da ake yi da kiran gwamnan jihar Kebbi a wayar Salula
- Matar mai suna Aisha Zakari tana kiran gwamnan na jihar na Kebbi a wayar ne tana tsorata shi
- Sai dai lauyanta ya bayyana cewa yanzu haka kotu ta bayar da belinta, sannan za a cigaba da sauraron kararta a karshen wannan watan
Wata mata da ake ta nemanta ruwa ajallo yanzu dai ta shiga hannu bayan, hukumar DSS sunje har gidan da take sun kamata, kamar dai yadda lauyanta ya yiwa manema labarai bayani.
Ga yadda hirar ta su ta kaya:
Dan jarida: Ranka ya dade zamu so mu samu cikakken sunanka, da kuma bayani akan matar da kake karewa?
Lauya: Sunana Barrister Bashir Umar, sunan matar da nake karewa Aisha Zakari, sannan kuma tuhumar ta ne ake yi, laifin da ake tuhumarta dashi shine tayar da hankalin gwamnan jihar Kebbi.
A ka'idar shari'a shine, wannan laifi da Aisha ta aikata ana iya bayar da belin mutum akan shi, saboda akwai sashe na 341 sakin layi na biyu, na shari'ar kasa da yace duk wanda ake tuhuma da laifi, indai har ba zai gudu ba, ko kuma ya bata binciken da ake yi masa ko kuma ya aikata wani laifi to ana iya bayar da belin shi.
KU KARANTA: Na rasa yadda zanyi da ita saboda har cikin dakin mu na sunnah Madina take kawo gardi tayi zina dashi - Wani mutumi ya koka
Akan haka kuwa wannan laifi da Aisha tayi ya cancanci a bayar da ita beli, saboda babu wata shaida da aka kawo da take nuna cewa Aisha ta aikata wannan laifi.
To Alhamdulillahi kotu ta bayar da ita beli, kuma ta bayar da dama cewa duk wanda bai aminta da wannan beli da kotu ta bayar ba yana iya daukaka kara, amma fa akwai wani abu, wannan matar da ake tuhuma da laifi tana da jaririya karama da bata wuce watanni biyar ba.
A karshe kuma kotu ta daga sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Satumbar nan da muke ciki.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng