Kotu ta kwace kujerar dan majalisa PDP a jihar Sokoto, ta bayar da umurnin yin zaben raba gardama

Kotu ta kwace kujerar dan majalisa PDP a jihar Sokoto, ta bayar da umurnin yin zaben raba gardama

- Kotun zabe da soke nasarar da Hon. Sahabi Umar na jam'iyyar PDP ya samu a zaben ranar 9 ga watan Maris na kujerar majalisa jihar na wakilcin mazabar Bunji

- Kotun ta soke zaben na sakamakon kara da Hon Bala Bature Mohammed na jam'iyyar APC ya shigar na kallubalantan zaben

- Kotu ta ce an saba wasu dokoki a zaben na baya kana ta bayar da umurnin sake yin zaben raba gardama a wasu rumfunan zabe hudu

Kotun sauraron karrakin zabe da ke zaman a Sokoto a ranar Talata ta bawa Hukumar zabe mai zaman kanta INEC umurnin gudanar da zaben raba gardama a rumfunan zabe hudu da ke mazabar Binji na zaben dan majalisar jiha.

Daily Trust ta ruwaito cewa Rumfunan zaben da za a yi zaben raba gardamar sun hada da Rumfar Marina da Kusa da Garkar Magaji a mazabar Maikulki sai kuma Shiyyar Sarkin Aski a mazabar Binji da Tumunin Magaji a mazabar Soron Gabas.

Alkalin kotun Mai shari'ar Hamman Idi Polycarp ya ce zaben bai kammalu ba yayin da ya ke yanke hukunci kan shari'ar da dan takarar jam'iyyar APC a zaben ranar 9 ga watan Maris, Hon Bature Mohammed Binji ya shigar na kallubalantar nasarar dan takarar PDP Hon. Sahabi Umar.

DUBA WANNAN: Nan da shekara 15 man fetur zai zama 'kayan kawai' - Gwamna Badaru

A cewarsa, akwai wasu dokokin zabe da aka saba kuma hakan ya shafi sakamakon zaben hakan yasa ya dace a gudanar da zaben raba gardama.

Mai shari'ar Polycarp ya ce tazarar da ke tsakanin Umar da ya samu kuri'u 11,995 da Bature da ya samu kuri'u 10,580 kawai 1,415 ne wadda hakan ya gaza adadin mutanen da su kayi rajista a mazabu hudun da aka samu matsalolin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel