Daukar dala ba gammo: Wani mutum ya naushi wata mai juna biyu a fuska

Daukar dala ba gammo: Wani mutum ya naushi wata mai juna biyu a fuska

Wani mutum mai shekara 35, Olatunji, wanda ake zargi da yiwa wata mai juna biyu naushi a fuska, ya gurfana a gaban kotun Majistare da ke Ogudu, Lagas a ranar Talata, 17 ga watan Satumba.

Olatunji na fuskantar tuhume-tuhume biyu na cin zarafi da kuma barazanar tayar da rikici.

Dan sanda mai kara, sufeto Donjour Pereze ya fada ma kotu cewa wanda ake karan ya aikata laifin a ranar 8 ga watan Satumba, da misalin karfe 4:00 na rana a yankin Alapere da ke Ketu na Lagas.

Perezi yayi zargin cewa wanda ake karan ya naushi wata mai ciki, Misis Yinka a fuska da kirji.

Dan sandan ya kuma yi zargin cewa mai laifin yayi barazanar yi mata asiri.

Laifin, a cewarsa ya Saba na sashi na 56 da 173 na dokar jihar Lagas na 2015.

Sashi 56 ya tanadi zaman gidan kurkuku na shekara uku ga mai laifin haka zalika sashi na 173.

Sai dai wanda ake karan bai amsa laifinsa ba.

Mai shari’a Bukola Mogaji ta bayar da belin mai laifin kan N100,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Kasar Iran tace ba za ta tattauna da Amurka ba

Mogaji ta kara da cewa dole wadanda za su tsaya masa su kasance da hujjar biyan haraji ga gwamnatin jihar Lagas.

Ta dage shari’an zuwa ranar 14 ga watan Oktoba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel