Taka leda: Najeriya za ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Brazil a Singapore

Taka leda: Najeriya za ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Brazil a Singapore

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles za ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Brazil a wani wasan sada zumunta da zai wakana a filin kwallo na kasar Singapore, kamar yadda rahoton jaridar Pulse ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar kwallon kafa ta Brazil, CFB, ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na yanar gizo a ranar Talata 17 ga watan Satumba, inda tace Brazil za ta buga wasannin sada zumunta guda biyu.

KU KARANTA: Gwamna Umahi zai nada mutane 800 a matsayin masu bashi shawara

Yan wasan Brazil zasu fara karawa da kungiyar kwallon kafa ta Sanigal ne a ranar 10 ga watan Oktoba, sa’annan ta kece raini da kungiyar Super Eagles a ranar 13 ga watan Oktoba a kasar Singapore.

Wannan shine wasan sada zumunta na biyu da Najeriya za ta buga tun bayan karawarta da kungiyar kwallon kafa ta Ukraine a ranar 10 ga watan Satumba, inda aka tashi wasa kunnen doki 2-2.

Haka zalika wannan wasa shine wasa na biyu da Najeriya zata hadu da kasar Brazil a matakin manyan yan kwallo, tun bayan wasan sada zumunta da suka buga a watan Yunin shekarar 2003 a yayin bude filin wasa na kasa dake Abuja, inda Brazil ta lashe da 3-0.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel