Yanzu Yanzu: Farasin kayayyaki ya sauka duk da rufe iyakar kasar – Hukumar kididdiga ta kasa

Yanzu Yanzu: Farasin kayayyaki ya sauka duk da rufe iyakar kasar – Hukumar kididdiga ta kasa

Hukumar kididdiga ta kasa a ranar Talata, 17 ga watan Satumba ta bayyana cewa farashin kayayyaki ya sauka daga kaso 11.08 bisa dari a watan Yuli zuwa kaso 11.02 bisa dari a watan Agusta.

Hukumar kididdigan a rahotonta ta bayyana cewa farashin kayayyaki na kaso 11.02 bisa dari na watan Agusta ya wakilci ragi na kaso 0.06 bisa dari na shekara-shekara.

Hukumar ta bayyana cewa saukar da farashin kayayyakin ya ci gaba a watan Agusta duk da sanarwar da aka sha yi game da sanya takunkumi akan shigo da wasu kayayyaki abinci, karancin albashi da kuma rufe iyakar kasar da aka yi kwanaki.

Game da tasirin rufe iyakar kasar akan farashin kayayyaki, hukumar kididdigan ta bayyana cewa ba lallai ne kasar ta ga wanni tasiri kan farashin ba a yanzu domin rufe iyakar ya shafi ranaku 11 ne cikin 31 a watan Agusta.

KU KARATA KUMA: NECO ta rike sakamakon jarrabawar dalibai 30,000 a Neja saboda bashi

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cwwa babban mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Ritaya Manjo Janar Babagana Monguno, yace iyakokin kasar za su ci gaba da kasance a rufe har sai an cimma manufofin da ke tattare da kulle su.

Monguno a fada ma manema laarai a karshen mako cewa aikin hadin gwiwa na tsaro da ke gudana wanda ya sanya aka rufe iyakokin zai fi kwanaki 28 da aka bayyana da farko sannan kuma zai ci gaba da kasancewa a haka har sai an cimma manufofi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel