An dakatar da wata budurwa ma'aikaciyar banki da tayi zina da maza sama da 200, bayan ta yi musu alkawarin nema musu aiki

An dakatar da wata budurwa ma'aikaciyar banki da tayi zina da maza sama da 200, bayan ta yi musu alkawarin nema musu aiki

- Wani babban banki na kasuwanci a kasar Zambiya ya dakatar da wata babbar ma'aikaciyar bankin

- Hakan ya biyo bayan kama ta da laifin yin zina da maza sama da dari biyu da tayi, yayin da take yi musu alkawarin nema musu aiki da basu bashi

- Asirin matar ya tonu ne bayan wasu maza sama da guda goma sun kai kararta akan alkawarin da tayi musu ta kasa cikawa bayan kuma sun biya mata bukatar ta

An dakatar da Wata budurwa ma'aikaciyar banki a bankin kasuwanci na kasar Zambiya, bayan an kamata da laifin kwanciya da maza sama da dari biyu (200), ciki kuwa hadda wadanda take yiwa alkawarin nema musu aikin yi.

Matar wacce aka bayyana sunanta da Mutale Winfridah babbar ma'aikaciya ce bankin kamar yadda jaridar ZambianObserver ta ruwaito.

An ruwaito cewa tana amfani da mukamin da take dashi a bankin wajen yiwa maza alkawarin basu aiki da kuma yiwa wasu alkawarin basu bashi, idan har suka yadda suka kwanta da ita.

KU KARANTA: Tirkashi: Iya wadanda ke da digiri a dakikanci da rashin hankali ne kawai zasu bar PDP su koma APC - Dino Melaye

An yanke hukuncin dakatar da matar ne mai shekar 39 wacce har yanzu ba ta yi aure ba, bayan wasu maza sama da guda goma sun kai kararta akan abinda tayi musu.

An ruwaito cewa taki yadda tayi aure ne bayan saboda tana so taga ta tara kwalayen makaranta kafin ta nemi miji tayi aure.

Bankin dai har yanzu bai sake wata magana akan ko akwai wani hukunci da zai dauka akan matar ba bayan dakatar da ita din da yayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng