Karkatar da albashin ma'aikata: EFCC ta cafke Abdullahi Sa'idu, shugaban SMA a Sokoto

Karkatar da albashin ma'aikata: EFCC ta cafke Abdullahi Sa'idu, shugaban SMA a Sokoto

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin (EFCC) ta cafke shugaban SMA (Sokoto Marshal Agency) bisa zarginsa da karkatar da kudin biyan albashin ma'aikata da yawansu ya kai miliyan N10.

Hukumar EFCC ce ta sanar da hakan ne ranar Litinin a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Tuwita.

A cewar sanarwar, jami'an hukumar EFCC reshen jihar Sokoto ne suka kama Sa'idu tare da akawun hukumar SMA, Bashar Dodo-Iya, ranar Juma'a ta makon jiya.

EFCC ta ce ta kama mutanen ne bayan ta samu korafi daga mambobi 39 na hukumar SMA a kan zargin abokan nasu biyu da karkatar da kudaden albashinsu, miliyan goma.

DUBA WANNAN: Mu na aiki tukuru domin farfado da tattalin arzikin Najeriya cikin kankanin lokaci kamar yadda China ta yi - Ministar Kudi, Zainab Ahmed

Masu korafin sun sanar da hukumar EFCC cewa shugaban hukumar da akawun sun gaza biyansu albashinsu na tsawon watanni uku ba tare da wani dalili ba.

Sun yi zargin cewa abokan aikin nasu sun karkatar da kudin biyansu albashi zuwa wasu harkokin na kashin kansu.

Hukumar EFCC ta ce binciken farko da ta gudanar ya tabbatar mata da cewa wadanda ake zargin sun karkatar da adadin kudaden da aka ambata.

Kazalika, hukumar ta bayyana cewa nan bada dadewa ba za ta gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel