Mu na aiki tukuru domin farfado da tattalin arzikin Najeriya cikin kankani lokaci kamar yadda China ta yi

Mu na aiki tukuru domin farfado da tattalin arzikin Najeriya cikin kankani lokaci kamar yadda China ta yi

Zainab Ahmed, ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, ta ce gwamnatin tarayya na aiki tukuru domin farfado da tattalin arzikin Najeriya cikin kankanin lokaci kamar yadda kasar China ta yi.

Da take magana ranar Litinin a wurin wani taro a Abuja, Zainab ta ce shirye-shirye sun yi nisa wajen kaddamar da wasu aiyuka da zasu saka Najeriya cikin jerin kasashen duniya 100 da yin kasuwanci ke da sauki.

Najeriya na mataki na 146 a cikin jerin kasashen duniya da yin kasuwaci ke da sauki a shekarar 2018 bayan ta fado daga mataki na 145 da take kai a shekarar 2017.

Ta bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta dauki matakan da zasu saka Najeriya ta zama abar kauna ga masu son saka hannun jari.

Ta ce daga cikin irin wadannan matakai akwai kafa hukumar saukaka yin kasuwanci PEBEC (Presidential Enabling Business Environment Council) domin bayar da tallafi ga duk wani yunkurin fadada harkokin kasuwanci.

Zainba ta ce matsayin Najeriya a jerin kasashen zai kara matsa wa sama da zarar gwamnati ta kaddamar da wadannan manufofi.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe Muhammad Bayero, basarake a karamar hukumar Mangu

"Mun kafa wasu kwamitocin bayar da shawara a kan tattalin arziki (SEZS) a sassa 6 na Najeriya domin mu hada kai da bangaren 'yan kasuwa masu zaman kansu.

"Manufar yin hakan shine yin koyi da abinda kasar China ta yi wajen bunkasa kasuwancinta cikin kankanin lokaci.

"Mun yi imani cewa idan aka kammala kaddamar da irin wadannan manufofi, harkokin kasuwanci zasu bunkasa, sannan aiyuka zasu samu, a cewar Zainab.

Kazalika, ta bayyana cewa gwamnati a shirye take domin hada gwuiwa da 'yan kasuwa a domin bunkasa bangaren sufuri da samar da kayan more rayuwa da zasu kara wa Najeriya farin jini a wurin masu son saka hannun jari.

Ta ce babban kalubalen da suke fuskanta shine karancin kudaden shigo wa da zasu bawa gwamnati damar kaddamar da aiyukan da take buri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel