Kuda wajen kwadayi ya kan mutu: Boka ya damfari wata matar aure naira miliyan 13

Kuda wajen kwadayi ya kan mutu: Boka ya damfari wata matar aure naira miliyan 13

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen babban birnin tarayya Abuja sun samu nasarar kama wani Boka, Muhammad Bako, tare da gurfanar dashi gaban wata babbar kotu dake Mpape a kan tuhumarsa da damfarar wata mata naira miliyan 13.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa ana tuhumar Bako da aikata laifuka guda uku da suka hada da hadin kai wajen aikata miyagun laifi, kwacen kudi da kuma barazana.

KU KARANTA: Akwai bukatar ku zage damtse a kan batun wutan lantarki – Sarkin Zazzau ga FG

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dansanda mai shigar da kara, A.O Oloafe ya bayyana ma kotu cewa wata mata mai suna Magret Igbinobaro ce ta kai karar boka Bako gaban hukumar tsaro ta sirri, NIA.

“Bokan, wanda kuma direban Tasi ne ya dauki Magret daga garin Minna na jahar Neja zuwa Abuja a ranar 25 ga watan Afrilu, a yayin haka ne Bako ya yi ma Magret cewa shi fa boka ne, kuma zai iya mata maganin duk wani abu dake damunta.

“Shi da kanshi ya tabbatar ma Yansanda a yayin bincike cewa ya yi ma Magret asiri ta biya kudi naira miliyan 13 zuwa asusun bankinsa na GtB, mai lamba 0259536443, inda yace ya yi amfani da kudin ne wajen gida gida. Sa’annan ya yi barazanar kashe Magret da zarar ta bayyana ma wani cewa ta bashi kudi.” Inji shi.

Dansandan yace laifukan da ake tuhumar boka Bako dasu sun saba ma sashi na 97, 293 da 397 na kudin hukunta manyan laifuka, sai dai boka Bako ya musanta aikata dukkanin laifukan.

Daga karshe Alkalin kotun, Hassan Muhammad ya bada belin Bako a kan kudi naira miliyan 30, tare da mutane biyu da zasu tsaya masa, sa’annan ya dage karar zuwa ranar 4 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel