Abin da zai faru idan Fulani su ka tafi yajin aiki – Inji 'Yar Miyetti Allah

Abin da zai faru idan Fulani su ka tafi yajin aiki – Inji 'Yar Miyetti Allah

Hajiya Baheejah Mahmood wanda ita ce shugaban mata na kungiyar nan ta Fulani watau Miyetti Allah na reshen jihar Bauchi ta yi wata hira da ‘yan jaridar Tribune a karshen makon nan.

A wannan tattaunawa da aka yi da Baheejah Mahmood, ta fito ta yi magana game da Makiyaya, shirin RUGA, kiwon dabbobi, da sauran abubuwan da su ka shafi Fulani da ke Najeriya gaba daya.

Jagorarar da kungiyar Miyetti Allah Kautal Hor ta fadawa ‘yan jarida cewa Makiyaya Fulani su na cikin masu taimakawa tattalin arzikin Najeriya, kuma sun taimaka wajen arahar nama da nono.

Bajeejah ta ce: “Fulani su na taimakawa tattalin arziki da mutanen Najeriya sosai. Su ne ke kawo kashi 90% na naman da ake ciki. Su ne ke kuma ba mu shanu, kaji, tsutsaye da awaki da tumaki.”

Shugabar matar na Miyetti Allah na Bauchi ta kara da cewa: “Su ne ke ba mu nono (madara), sannan su kawo mana fatu a kasar nan wanda ke karfafawa GDP na tattalin arzikin Najeriya.”

Ba a nan kurum gudumuwar Makiyaya Fulani ta tsaya ba domin Baheejah Mahmood ta ce saboda rawar ganin su ne ake samun nama da kuma kwai a cikin araha daga dabbobin da su ke kiwo.

KU KARANTA: An gano Boko Haram sun kawo sabon salon a yakin da ake yi har gobe

Hajiya Mahmood ta bayyana cewa a lokacin bukukuwan Idi da Kirismetin Musulmai da Kiristoci, ana samun naman dabbobi irin su tinkiya da awaki da rago da za a yanka ne saboda Makiyaya.

Babbar Jagorar Fulanin ta ce jama’a za su gane amfanin Makiyaya Fulani ne idan su ka dauki ko da mako guda rak ba tare da sun zo kasuwa ba. Baheejah tace lokacin za a gane amfaninsu.

Ban da irin wahalar da Makiyan na Fulani su ke sha, shugabar wannan kungiya ta bayyana cewa babu wani abin da Fulanin su ke amfani da shi daga gwamnati na asibiti ko hanya ko ruwan sha.

Wannan Baiwar Allah ta ce kafin a ba Fulani Makiyaya wutar lantarki ko wani abin more rayuwa, sai sauran kusan duka gama-garin kasa sun samu don haka ta nemi a kawo gyara da sabon tsari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel