A kalla soji 13 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Boko Haram na kwanakin nan

A kalla soji 13 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Boko Haram na kwanakin nan

- A kalla soji 13 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da Boko Haram suka kai a kwanakin nan

- Majiya daga rundunar ta sanar cewa tun daga ranar Lahadi da ta gabata ake abu daya

- Majiyar tace 'yan ta'addan sun kai hari Gubio, Gajigana da Gajiram inda suka kashe wasu sojin tare da yin awon gaba da kayayyakin aikin sojin

A kalla sojin Najeriya 13 suka rasa rayukansu a kwanaki kadan da suka gabata. Sun rasa rayukansu a harin da 'yan Boko Haram me kaiwa rundunar sojin a gabas maso arewan, inji majiya daga rundunar.

Maharan sunyi gaba da kayayyakin aikin sojin masu yawa.

Rundunar sojin sunki sanar da hare-haren da aka fara tun a ranar Lahadi da ta gabata.

Mai magana da yawun sojin Najeriyan, Sagir Musa, ya ki tofa albarkacin bakinsa akan tambayoyin da manema labarai suka masa a ranar juma'a game da hare-haren.

Amma wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta, daga rundunar sojin ta sanar da jaridar Premium Times cewa: "Kwanakin da suka gabata basu zama masu sauki ga rundunar ba."

"Rundunarmu da ke sintiri kusa da Gajigana sun ci karo da 'yan ta'addan inda da yawa suka rasa rayukansu," yace.

KU KARANTA: Tirkashi: Ya kashe matarsa har lahira akan kin shayarda jinjirinsu

Majiyar tace, rundunar da ke Gudumbali ma sun cin karo da 'yan ta'addan da suka bayyana a motocin yaki.

Majiyar tace, lamarin ya auku ne wajen karfe 5 na yammacin ranar Lahadi wajen titin Gurunda zuwa Zari. Sojoji kusan 100 ne suka samu tserewa zuwa Damasak bayan 'yan kwanaki.

"A yanzu maganar da muke yi, sojoji 7 ne aka tabbatar da rasuwarsu. Amma zai iya yuwawa sunfi hakan saboda 'yan ta'addan sun yanka wasu sojojin, wasu kuma sun daura igiya a wuyansu tare da jansu a motocin yakinsu," inji shi.

A ranar Laraba, yayin da sojin runduna ta 7 ke makokin mutuwar abokan 'yan aikinsu, an kara kai hari a Kukawa.

Duk da ba a samu wanda ya rasa ransa ba, "Sun zo dibar kayan aiki ne, wanda suka diba tare da yin gaba da su."

An kara kawo hari a yammacin ranar Alhamis a Gubio wanda a lokaci daya aka kai hari Gajiram da Gajiganna.

Majiyar race an kashe sojoji 6 da kuma wani Dan taimakon kai da kai 1 a harin Gubio inda maharan suka yi awon gaba da motocin yaki uku da motar sintiri daya.

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai, a ranar Juma'a yaje Maiduguri inda yayi taron sa'o'i da kwamandojin rundunonin a hedkwatar 'Operation Lafiya Dole' da ke Maiduguri.

Shugaban sojin dai bai yi magana da manema labarai ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel