Trump ya tabbatar Amurka tayi nasarar kashe Hamza bin Laden

Trump ya tabbatar Amurka tayi nasarar kashe Hamza bin Laden

- Shugaban Amurka Donal Trump ya tabbatar da mutuwar dan Osama bin Laden

- Marigayi Hamza ya maye gurbin mahaifinsa Osama bin Laden da aka kashe lokacin mulkin Shugaba Obama

- A cewar Shugaban na Amurka, an kashe Hamza ne yayin wani hari da dakarun Amurka suka kai a kan iyakar Afganistan da Pakistan

Shugaba Donald Trump na Amurka a ranar Asabar 14 ga watan Satumba ya tabbatar da kisar Hamza bin Laden, dan tsohon shugaban kungiyar Al-Qaeda Osama bin Laden kamar dan jaridar White House Zeke Miller ya sanar a Twitter.

A cewar shugaban kasar ma'abocin shafin twitter, an kashe Hamza ne yayin wani harin kawar da 'yan ta'adda da aka kai a kan iyakar kasar Afganistan da Pakistan.

"Rashin Hamza bin Laden ya karya gwiwar Al-Qaeda saboda sun rasa shugaba duba da irin dangantakar da ya ke dashi da mahaifinsa kuma hakan zai kawo cikas ga ayyukan kungiyar," a cewar Shugaban na Amurka cikin wata sanarwa ta White House ta fitar.

Shugaba Trump ya kara da cewa "Hamza bin Laden ya kasance jigo wurin hadin gwiwa da wasu kungiyoyin ta'addanci masu yawa,"

DUBA WANNAN: An bawa wani mai sukar gwammatin Buhari mukami a gwamnati

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel