'Yan sanda sun kama 'yan Shi'a 8 da wasu mutum 26 a jihar Sokoto

'Yan sanda sun kama 'yan Shi'a 8 da wasu mutum 26 a jihar Sokoto

- Hukumar 'yan sanda ta jihar Sokoto ta kama 'yan Shi'a 8 da wasu mutane 26

- Tana zarginsu ne da tada zaune tsaye a jihar

- Hukumar ta bayyana yadda suka kai hari ga 'yan sanda tare da kwace bindiga daya daga hannun wani Dan sanda

Kaoje yace a ranar 10 ga watan Satumba, 'yan kungiyar IMN wadanda aka fi sani da 'yan shi'a sun take dokar gwamnatin tarayya ta hanyar fitowa don tattakin ranar Ashura

"Sun fito daga karamar hukumar Illela don yin taron Ashura wanda a wajen ne suka hari Dan sanda har suka kwace bindiga daga hannunsa. Bayan hukumar 'yan sandan sun samu rahoton abinda ya faru, sai aka tura 'yan sanda wajen 'yan kungiyar inda suka kama mutane 8 tare da karbo bindigar," inji shi.

Yace hukumar 'yan sandan ta kama wasu mutane 2 da take zargin; Saifullahi Aminu da Yusuf Maidamma akan zargin hada kai don cuta, safarar mata da kisa.

KU KARANTA: 'Yan Shi'a sunyi jana'izar mutanen da suke zargin 'yan sanda da kashe musu

"A ranar 31 ga wata ne, wata Sadiya Adamu ta kawo karar Saifullahi Aminu da Yusuf Maidamma, da hada kai wajen yaudarar kanwarta Khadija Adamu mai shekaru 26."

"Sun bata magani don gusar mata da hankali Inda suka ba wani Abdullahi Bafarawa da Shamsudeen Lawal don lalata da ita."

"An hanzarta kaita asibiti a nan cikin Sokoto a ranar 30 ga watan Augusta inda ta rasu a ranar 4 ga watan Satumba."

"Tuni dai an kama wadanda ake zargin Inda ake kokarin kama sauran wadanda ake zargin," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel