To fah: A karon farko Jarumi Ali Nuhu yayi magana kan kamen da hukumar fina-finai take yi

To fah: A karon farko Jarumi Ali Nuhu yayi magana kan kamen da hukumar fina-finai take yi

- A karon farko jarumi Sarki Ali Nuhu yayi magana akan kamen jaruman da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano keyi

- Jarumin ya bayyana cewa yana rokon hukumar da tayi duba zuwa ga lamarin a yiwa jarumi Nazir Sarkin waka sassauci

- Haka kuma daukacin mutane suna ganin cewa akwai siyasa a cikin wannan al'amari duba da yadda ba a taba kama wani dan APC ba sai iya 'yan Kwankwasiyya kawai ake kamawa

Jarumia Ali Nuhu ya sanya baki akan batun da ake ciki na kama mawaki Nazir Ahmad Sarkin Wakar Sarkin Kano, inda yayi kira ga hukumar kan tayi sassauci ga mawakin inda ya wallafa a shafinsa cewa:

"Rokona ga hukumar tace fina-finai ta jihar Kano shine a dubi al'amarin naan ayi sassauci ga kaninmu kuma abokin sana'armu Sarkin wakar San Kano. Allah ya kawo maslaha cikin gaggawa, amin,"

Daukacin mutane na ganin kama Nazir da akayi yana da alaka da siyasa sai dai abin mamaki 'yan fim din dukannin su da masu goyon bayan ra'ayin Kwankwasiyya da masu goyon bayan Gandujiyya sun hada baki wajen kira da a saki Mawakin.

KU KARANTA: Sai kace karya: Nayi zina da mutum sama da 700, 27 daga cikinsu duk 'yan fim ne da mawaka - In ji wata Slay Queen

Misali Ali Nuhu, Nuhu Abdullahi, Abdul'amat mai kwashewa, Nazir dan Hajiya, da sauran jiga-jigan 'yan Kannywood dake jam'iyyar APC sun koka kan kama Nazir din, inda suka yi ta wallafawa a shafukansu na Instagram suna kira da a sake shi, amma duk da haka al'umma na cigaba da tabbatar da cewa da siyasa a cikin lamarin duba da cewa ba a taba kama dan jam'iyyar APC ba sai mabiyan Kwankwasiyya.

Jaruma Teema Makamashi jakadiyar FKD ita ma tayi video cikin nuna alhini inda ta nuna bacin ranta kan kama Nazir din da aka yi har ta yi ikirarin ita ma ta kusa tabi sahun abokan sana'arta da suka fice daga kungiyar shirya fina-finan ta Kannywood saboda ta gaji da abinda ke faruwa a masana'antar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng