Shugaba Mnangagwa ya sanar da wurin da za a binne Mugabe

Shugaba Mnangagwa ya sanar da wurin da za a binne Mugabe

Za a binne tsohon Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe a filin binne jarumai na kasa (National Heroes Acre) a watan Oktoba kamar yadda Shugaban kasa Emmerson Mnangagwa ya fadi a ranar Juma'a.

Kafin Shugaban kasar ya yi wannan jawabi, gwamnatin Zimbabwe da iyalan Mista Mugabe ba su cimma matsaya kan wurin da za a binne tsohon shugaban kasar ba.

Da farko an amince cewa za a yi masa jana'iza irin ta muhimman mutane ne a ranar Lahadi a Hiltop Shrine da ke Harare amma mai magana da yawun iyalan Mugabe, Leo Mugabe ya shaidawa manema labarai cewa an soke wannan tsarin.

Za a kai gawar marigayi Mugabe kauyensu na Zvimba a ranar Lahadi domin yi masa wasu addu'o'i na gargajiya kafin daga bisani a binne shi kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Nasarar Buhari a kotu: Wani dan PDP ya cakawa dan APC kwalba

Za a binne Mugabe a National Heroes Acre a watan Oktoba a cewar Mista Mnangagwa.

An dawo da gawar Mugabe daga kasar Singapore ne a ranar Laraba inda ya rasu yana da shekaru 95 a duniya.

Ya tafi kasar ta Singapore ne inda ya dauki lokaci yana jinyar wata cuta da ba a bayyana ba tun watan Afrilu.

An hambarar da shi daga karagar mulki ne a shekarar 2017 bayan ya shafe kusan shekaru 40 a kan karagar mulki.

Yayin da wasu ke girmama shi saboda gwagwarmayar da ya yi a kan turawan mulkin mallaka, wasu na kyamarsa inda suke ganin shine ya lalata tattalin arzikin Zimbabwe kuma yana yi wa abokan hamayya matsin lamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel