Mahaifina ya tsine min saboda naki yarda da mijin da ya zaba mini

Mahaifina ya tsine min saboda naki yarda da mijin da ya zaba mini

- Ladidi ta bayar da labarinta cikin kuka mai ban tausayi

- Ta bayyana yadda mahaifinta ya nuna rashin amincewar shi akan mijin da ta nuna tana so ta aura

- Ta ce bayan ya nemi ya aura mata wani sai ta kai karar shi wajen hukumar Hisba, sune suka shiga maganar

"Ana gobe za a daura mini aure, na je na samu mahaifinmu na bukaci ya bani kudi zanje nayi lalle sai yake fada mini ai banda ni a daurin auren. A cikin daren ranar ya kara kirana yake fada mini na shirya da safe zamu je ayi mini gwaji saboda za a daura mini aure da wani.

"Ni kuma gaskiya bana son mutumin da zai aura mini, mahaifiyata ta goyi bayana muka je wajen hukumar Hisba aka warware maganar auren," in ji Ladidi.

Ladidi dai yarinya ce karama mai shekaru 16 a duniya kasancewar yanzu kowacce mace a yankin karkara da ta fara tasawa sai ayi mata maganar aure.

Masoya sun yiwa Ladidi ca a ka, haka yasa ta fitar da mutum daya da take so ta aura iyayenta suka sanya baki a maganar har aka sanya ranar daurin aure.

Saura kwana daya a daura aure, sai mahaifinta mai suna Malam Ali ya bayyana cewa ya canja shawara, ma'ana ya fasa bayar da ita ga wanda ta nuna tana so, inda yace yayi mata sabon zabi, hukuncin da ita yarinyar ta ce tayi fatali dashi kenan kamar yadda ta bayyanawa jaridar BBC Hausa.

Hakan yasa Ladidi da mahaifiyarta suka garzaya wajen hukumar Hisba ta jihar Jigawa domin ta sanya baki a kan lamarin.

KU KARANTA: Wata sabuwa: A tura sojoji mata su yaki 'yan ta'adda tunda mazan sun kasa tabuka komai - Aisha Buhari

Hukumar ta sanya baki akan lamarin, daga karshe ta sanya mijin da aka daura mata auren dashi ya sake ta.

Sai dai kuma mahaifin Ladidi ya karyata kalaman da 'yarsa ta bayar. Ya ce ana saura sati biyu a daura auren mahaifiyar Ladidi ta sauya magana, ta bayyana cewa bata son Ladidi ta auri mijin da tace tana so.

Ya kara da cewa tayi hakane domin tana so Ladidi ta auri wani dan uwanta.

Lokacin da ya kamata Ladidi ta kasance cikin farin ciki da jin dadi saboda an raba ta da wanda bata so, sai aka samu akasin haka domin kuwa ta shiga cikin kunci da fargaba, saboda mahaifinta yayi wani furuci marar dadin ji, ma'ana ya tsine mata.

"Duk abinda nayi mata daga lokacin da aka dauki cikinta zuwa yau ban yafe mata ba. Na ce taje ta auri duk wanda take so. Sannan kuma na sake daukar mataki duk cikin 'yan uwana babu wanda zai je daurin aurenta," a cewar mahaifin yarinyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel