Budurwa yar Kaduna ta gamu da hukuncin bulala 80 saboda shan tabar wiwi

Budurwa yar Kaduna ta gamu da hukuncin bulala 80 saboda shan tabar wiwi

Wata budurwa yar shekara 19 ta gamu da fushin kotu bayan an gurfanar da ita gaban kotun kan tuhumarta da ake yi ta’ammali tare da sha da busa tabar wiwi a bainar jama’a, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito budurwar mai suna Zainab Abdullahi ta gurfana ne gaban kotun shari’ar Musulunci dake unguwar Magajin Gari cikin garin Kaduna, inda ta amsa tuhumar da ake yi mata.

KU KARANTA: Matsalar tsaro: Red Cross ta bayyana yan Najeria 22,000 da ba’a san inda suke ba

Bayan ta amsa laifin na ta ne sai Alkalin kotun, mai sharia Malam Muhammad Shehu Adamu ya yanke mata hukuncin bulala guda dai dai har guda 80, kamar yadda yace wannan shine hukuncin da dokar Musulunci ta tanadar ma duk mai shan kayan maye.

Da fari, dansanda mai shigar da kara, Ibrahim Shuabibu ya bayyana ma kotun cewa an kama Zainab ne a daidai lokacin da take shan tabar wiwi a kan titi a bainar jama’a.

Haka zalika Dansandan ya bayyana ma kotu cewa dama can an taba Zainab da wani laifi wanda har aka yanke mata hukuncin zaman gidan yari sakamakon ta gaza biyan kudin tara N7,000.

A wani labarin kuma, Wata kotu dake zamanta a jahar Kano ta bada belin fitaccen mawakin Hausan nan, kuma sarkin wakan Sarkin Kano, Naziru M Ahmad, amma fa bisa wasu tsauraran sharudda guda uku.

Idan za’a tuna hukumar tace fina finai ta jahar Kano ta samu nasarar kama shahararren mawakin, kuma sarkin mawakan mai martaba Sarkin Kano, Naziru M Ahmad ne da yammacin Laraba, 11 ga watan Satumba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel