Da dumi dumi: Kotu ta bayar da belin Naziru Sarkin waka a Kano

Da dumi dumi: Kotu ta bayar da belin Naziru Sarkin waka a Kano

Wata kotu dake zamanta a jahar Kano ta bada belin fitaccen mawakin Hausan nan, kuma sarkin wakan Sarkin Kano, Naziru M Ahmad, amma fa bisa wasu tsauraran sharudda guda uku, inji rahoton BBC Hausa.

KU KARANTA: Shari’ar zaben Sanata: Kai ya rabu game da nasarar ministan Buhari a kotu

Idan za’a tuna hukumar tace fina finai ta jahar Kano ta samu nasarar kama shahararren mawakin, kuma sarkin mawakan mai martaba Sarkin Kano, Naziru M Ahmad ne da yammacin Laraba, 11 ga watan Satumba.

Hukumar ta kama Nazirun ne bisa tuhumar da take masa na sakin wata waka ba tare da tantance wakar ba, kuma ba tare da izininta ba, sai dai a yanzu majiyar Legit.ng ya bayyana cewa wakokin da ake tuhumar Nazirun da saki ya sakesu ne tun shekaru 4 da suka gabata.

Wadannan wakoki da ake tuhumarsa a kai sune Gidan Sarauta da kuma Sai dai Hakuri. Toh amma dai kotu ta bada belinsa a ranar Alhamis, inda ta gindaya masa sharudda guda uku kwarara wanda sai ya cikasu za’a samu yancinsa.

Wadannan sharudda dai sun hada da mika fasfonsa na tafiye tafiye ga kotu, gabatar da mutane uku da zasu tsaya masa wanda daga ciki akwai dagacin unguwarsa da ma’aikatan gwamnati guda 2 sai kuma na karshe zai biya kudi N500,000.

Da yake zantawa da majiyarmu, kaakakin Yansandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da cewa sun kama Naziru ne saboda amfani da kalaman batanci da ya yi a cikin wakokin. Shi ma dan uwan Naziru, Aminu Saira ya tabbatar da kama Nazirun, amma yace Yansanda sun fada musu gwamnati ce ya sanya su kama shi.

“An kama Naziru ne saboda fitar da wani kundin waka da ya yi mai suna ‘Gidan Sarauta’ da kuma ‘Sai Hakuri’ mun yi kokarin samun belinsa tun a daren Laraba, amma suka ki, Yansanda sun yi bincike a gidansa amma basu dauki komai ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng