Kama Naziru sarkin waka: 'Yan Kannywood sun mayar da martani

Kama Naziru sarkin waka: 'Yan Kannywood sun mayar da martani

Jaruman Kannywood da sauran masu ruwa da tsaki a harkar fina-finan sun fara tofa albarkacin bakinsu kan kama fitaccen mawaki, Naziru M. Ahmad sarkin wakan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

A jiya Laraba, rundunar 'yan sanda reshen jihar Kano ta ce ta kama mawakin ne saboda furta wasu kalmomin batanci da ya yi cikin wasu wakokinsa.

Ta kara da cewa za a gurfanar da shi a gaban kuliya a ranar Alhamis.

Sai dai dan uwan mawakin mai suna Malam Aminu Saira ya shaidawa BBC cewa gwamnatin jihar Kano ce ke yi wa mawakin bita da kuli saboda dalilan siyasa hakan yasa ta sa a kama shi ta hannu hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

DUBA WANNAN: Wani mutum da ya yi sojan gona a matsayin CP ya damfari sanatan arewa N1.8m

Kawo yanzu gwamnatin jihar Kano bata magana ba kan wannan zargin da aka yi mata.

Naziru M. Ahmed dai mabiyin akidar Kwankwasiyya ne kuma ya dade yana wakoki na kushe wasu abubuwa da gwamnatin APC ke yi a kasar.

Wasu daga cikin 'yan Kannywood sun tofa albarkacin bakinsu kan lamarin a shafukan su na sada zumunta.

'Yan Kannywood da suka bayyana ra'ayoyin su kan batun sun hada da Jaruma Hadiza Gabon, Jarumi Ali Nuhu, Mai bayar da umurni kuma jarumi, Falaku Dorayi, Nazifi Asnanic da sauransu.

Kama Naziru sarkin waka: 'Yan Kannywood sun mayar da martani
Kama Naziru sarkin waka: 'Yan Kannywood sun mayar da martani
Asali: Instagram

Kama Naziru sarkin waka: 'Yan Kannywood sun mayar da martani
Kama Naziru sarkin waka: 'Yan Kannywood sun mayar da martani
Asali: Instagram

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel