Toh fah: Wani mutum ya kai karar zakara kotu

Toh fah: Wani mutum ya kai karar zakara kotu

- Wani mutum Dan kasar Faransa ya maka zakara a kotu

- Yayi hakan ne sakamakon damunsa da cara da yayi ikirarin zakaran na yi

- Tuni dai alkali ya wanke zakaran tare da cin tarar Pam 1,000 ga mai karar

Wani mutum Dan kasar Faransa, mai suna Jean-Louis Biron ya shigar da karar wani zakara mai suna Maurice akan damunsa da yake da carar sassafe.

Biron mazaunin birnin Rochefort, ya kai korafinsa ne akan tsuntsun mai shekaru 4 a duniya gaban kotu.

Amma kuma, kotun ta soke karar akan carar sassafen tare da umartar mai karar da biyan mai zakaran Pam 1,000 wanda tayi daidai da Naira 399,275 na barnar da aka yi masa.

Hargitsin wanda ya dau tsawon shekaru biyu ya kawo karo tsakanin rayuwar zamani da al'adun da.

KU KARANTA: Musayan fursunoni: Yayinda gwamnatin Katsina ta saki yan bindiga 6, su kuma sun saki mutane 20 sa suka sace

"A yau dai Maurice ya ciyo wa dukkan kasar Faransa yaki," Corrine Fesseau, mai zakaran ya ce.

Biron ya fara korafi akan carar Maurice ne ga masu zakaran; Jacky da Corrine Fesseau, amma suka ki rabuwa da zakaran.

"Carar zakaran na farawa ne daga karfe 4:30 na asuba kuma yana cigaba ne har safe, zuwa rana," Biron ya rubuta a wasikar da ya aika ga makwafcinsa a 2017.

Da kuwa Maurice ya cigaba da cara, sai Biron ya tafi gaban kuliya don ta kwatar masa hakkinsa.

Anta labarin shari'ar a manyan jaridun kasar Faransar, har ma ta kai ga anyi riguna na siyarwa don kara ga zakara Maurice.

Ba haka ta tsaya ba, wasikun goyon bayan zakara Maurice sun ta isa kasar Faransa daga wurare da dama, har da Amurka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel